Boyayyar Taska



Ahlul Baiti (A.S) Su Ne Makoma

 Haka nan mummunan tunani da wadancan dauloli suka bari kuma suka gadar da shi ga wannan al’umma suka cigaba da yawo da zagayawa a kwakwalen ‘ya’yan wannan al’umma tamu, alhalin su wadannan soke-soke a kan tafarkin Ahlul Bait (A.S) da mabiyansu tun asali sarakuna sun assassa su ne domin tabbatar da mulkinsu, amma abin takaici sun wanzu a kwakwalen miliyoyin mutane har zamaninmu wannan.

Kuma sun ci gaba da zama dalilin takurawa mai tsanani a kan mabiya Ahlul Baiti, amma duk da haka mabiyansu sun ci gaba da wanzuwa a bayan kasa da yada haskensu. Al’amarin ya ci gaba har ya zama akwai lokacin da suka zama su ne rabin al’umma a bayan kasa!

Wani abin da zamu yi lura a kansa shi ne; da yawa daga malaman mazhabobin Ahlussunna sun yi karatu ne wajan Ahlul Baiti (A.S). Maliku ya yi karatu wajan Imam Sadik, haka ma Abu Hanifa, har ma Abu Hanifa ya kasance yana cewa: “Ba don Shekara biyu ba da Nu’uman ya halaka” wato; Ba don karatun shekara biyu da ya yi a wajan Imam Ja’afa Sadik (A.S) ba da ya halaka”[9].

Maliku yana cewa: “Ya kasance ya ga Imam Ja’afar (A.S) mai yawan murmushi da fara’a amma idan aka ambaci Manzon Allah (S.A.W) a gabansa sai launinsa ya koma yalo (saboda girmamawa da shauki), ya ce: Ban taba ganin ya bayar da hadisin Manzon Allah ba sai yana da tsarki”[10]. Wannan kuwa lokacin da yake bayar da amsar dalilin da ya sanya shi girmamawa ga hadisan Manzon Allah (S.A.W) da tasirantuwar da ya yi daga imam Sadik (A.S). Wannan al’amarin yana nuna cewa Imam Assadik (A.S) ya yi masa tasiri wajan sanin Manzon Allah (S.A.W) da kuma girmama Hadisansa. Yayin da kuma shi Shafi’i ya kasance Dalibin Muhammad Dan Alhasan ne, wanda shi ne mutum na uku a Hanafiyya da shi ne ya rene shi, kuma Shafi’in ya gaji littattafan Muhammad Dan Alhasan ne, wanda shi kuma salsalar malamansa tana tukewa zuwa ga Imam Ali (A.S) ne.

Ya Musulmi Hattara Da Makiya!

A takaice dai mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) su ne mutanen da suka fi kowace jama’a dadewa karkashin farfaganda da karairayi na masu gaba da su a Tarihin dan Adam, kuma sun yi imani da Imamin wannan zamani Imam Mahadi (A.S) da musulmi suka hadu a kan cewa; zai bayyana ya kuma cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci.

Tambaya a nan shi ne, Shin idan Imam Mahadi (A.S) ya bayyana zai bar koyarwar kakanninsa ne ya riki wata koyarwa daban ko kuwa?. Wannan wani abu ne da dukkan musulmi suka hadu a kan rashin yiwuwarsa, kuma an sani cewa ba yanda za a yi ya bar koyarwar kakarsa Sayyida Zahara (A.S) da kuma Iyayensa (A.S), hasali ma shi Imami ne daga Imaman Wannan Gida, kuma yana da wata daraja ta musamman da ba wanda Allah ya yi wa ita, domin Annabi Isa (A.S) zai zama cikin rundunarsa karkashin umarninsa kuma ya rika yin salla a bayansa, kuma shi ne wanda zai zo ya cika duniya da haske da shiriyar musulunci ya tumbuke duk wani munafunci da duk sabani, ya zama ba abin da zai iko sai Addinin Allah.

Da yawa mutanen da aka haramta musu ni’imar shiriya ta Ahlul Bait (A.S), wasu farfaganda ta haramta musu karanta littattafansu ne ko sauraronsu, har yanzu a wata kasa a Gabas ta tsakiya da aka fi ko’ina danne hakkin dan Adam hatta a cikin Jami’a an hana kowane dalibi karanta littattafan mazhabar Ahlul Baiti (A.S). akwai wasu wasu mutane da su suna son su ji ko su karanta domin suna son musulunci, kuma suna son fahimtarsa da fadi ba da tsukakkiyar kwakwalwa da tsukakken tunani ba, sannan hankalinsu yana tambayar su cewa: Shin zai yiwu Manzo (S.A.W) ya tafi ya bar duniya ba tare da ya sanya magajinsa, halifansa, wasiyyi, da zai bari bayansa ba! alhali wannan shi ne sakon Allah na karshe! ga shi kuwa hatta idan zai tafi yaki sai ya bar wani mai tsaron gari? Wannan wata tambaya ce da take tasowa a tunanin mutane masu hankali da lura. Wasu masu tunanin suna dada tambayar kawukansu a kan wasu al’amura da suke damunsu kamar haka;

1.      Shin Fadima (A.S) zai yiwu ta ki yarda da halifan lokacinta ta kuma yi fushi da shi da zafafawa kamar haka ba tare da ta dogara da dalili na gaskiya ba?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next