Boyayyar Taska



Tsawon rayuwarsa: Rayayye ne boyayye daga ganin mutane, zai fito karshen zamani da umarnin Allah (S.W.T) domin ya cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci, muna rokon Allah ya gaggauta bayyanarsa.

Tsawon Imamancinsa: Yana da tsawo, har yanzu yana raye. Buyansa: Yana da buya biyu:

 1-Karami: Yana da tsawon shekara 74, ya fara daga shekarar 260 H har zuwa shekarar 329 H.

2-Babba: Ya fara daga shekarar 329H bayan mutuwar jakadansa na karshe har zuwa wannan zamanin.

Jakadunsa: Su hudu ne, su ne mutane suke karbar hukunce-hukuncensa daga gare su a lokacin buyansa karami. Wadannan jakadon su ne; 1-Usman dan Sa’id 2-Muhammad dan Usman 3-Husaini dan Ruhu 4-Ali dan Muhammad Assimiri. Alamomin bayyanarsa: Ba zasu kirgu ba sai dai zamu kawo guda hudu a nan: 1-Fitowar Sufyani 2-Kashe Al-Hasani 3-Zuwan Tutoci Bakake daga Khurasan 4-Fitowar Al-yamani.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:

Littafin Salim bn Kais

Tarihin Damishka

Fara’idus Simdaini



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next