ZamaninJuyin Juya Hali



Haka nan juyin imam Mahadi (A.S) wani juyi ne da ba a iya kwatanta shi da wani juyi na dan Adam, kamar juyin Faransa da da na Rasha, da na Cana, kamar yadda ba a iya kwatanta shi da wani juyi ta fuskancin tunani. Misali demokradiyyar jari-hujja an kafa ta a kan daidaito tsakanin mutane wanda ba ta iya samar da komai ba a wannan fage, kuma dalilin asalin rashin cin nasarar ta ya faru ne daga gabar da take yi da addini. Amma juyin imam Mahadi (A.S) ya doru kan asasin addini ne, kuma zai samar da ‘yancin daidaito na hakika da adalci ga kowane mutum.

Kuma a bisa dabi’a addinin duniya wanda bai kebanta da wani bangare ba shi ne zai iya kawo sauyin duniya, wannan addini kuwa a mahangar Shi'a shi ne addinin musulunci wanda yake kunshe da asasosin dukkan addinan ubangiji, kuma gurbata ba ta same shi ba, kuma kalubalen da kur’ani ya yi har yanzu wani addini bai ba shi amsa ba, don haka shi ne addini tsantsa a wajen Allah: “Hakika addini a wajan Allah shi ne musulunci” (Ali imran: 19).

Da fadinsa: Duk wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, ba za a taba karba daga gareshi ba (Ali imran: 85).

Da fadinsa: Allah yana umarni da adalici da ihsani (Nahal: 90).

Da fadinsa: Idan kun fada to ku yi adalci (An’am: 152).

Da fadinsa: ku yi adalci shi ne ya fi kusa da takawa (Ma’ida: 8).

Da fadinsa: Hakika mun aiko manzannnimu da hujjoji kuma muka saukar da littafin da ma’auni tare da su domin mutane su tsayu da adalci (hadid: 25)

Wani muhimmin abu kuwa shi ne a mahangar musulunci; duk inda mutane suke rayuwa a kowane yanki ne na duniya, da kowane irin yare ne suke magana, da kowace al’umma ce da kalar ko launin fatarta, dukkansu dangi daya ne, kuma sun zo daga asali daya na uwa da uba daya, kuma a girmamawar mutumtakarsu duka daya ne[41]. Don haka ne maganar kallafa musu aiki ta fuskantarsu bisa daidaito, da cewa: “Ya ku mutane”, ko kuma “Ya ‘yan Adam”. Kur’ani ya yi kakkausan suka game da kabilanci, da bambancin launin fata:

“Ya ku mutane mu mun hallice ku daga maza da mata, muka sanya ku jama’u da kabilu domin ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi takawarku” (Hujurat: 13).

Hadisin Manzon Allah a hajjin bankwana yana cewa: “Ya ku mutane ku sani ubangijinku daya ne, kuma hakika babanku daya ne, ku saurara ku ji, babu fifiko ga balarabe a kan ajami, ko ajami a kan balarabe, ko ja a kan baki, ko baki a kan ja sai dai da takawa”[42].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next