ZamaninJuyin Juya Hali



Wani muhimmin abu shi ne; bayyanar Dujal makaryaci mai sihiri mayaudari, koda yake wadansu mutanen sun fassara shi da cewa abin da yake nufi shi ne yaudarar yammacin duniya, suna ganin cewa Dujal ba wani mutum ayyananne ba ne[27], don haka kawar da Dujal ba zai yiwu ba da kawar da mutum daya.  Saboda haka yana bukatar tunani mai fadi da karfin soja domin fuskantar da duniya zuwa ga adalci, wannan kuwa al’amari ne da yake wuyan shugaban duniyar karshen zamani[28].

Haka nan ya zo cewa; Dujal azzalumi zai tara runduna sama da mutane 70 000 daga yahudawa, sannan kuma ya yi da’awar ubangijintaka. An ce zai bayyana yayin da imam Mahadi (A.S) ya yi nasara a kan Sufyani zai bude Istambul, sai imam (A.S) ya fuskanci Falasdin domin rushe asasin fasadi daga gabas ta tsakiya, ya fuskanci garin Akka, domin ya bude sauran kasashen Afrika ta hanyar Misira[29].

Bayan faruwar abubuwa masu yawa sai Annabi Isa (A.S) ya sauko a garin Kudus (Baitul mukaddas) domin ya taimaki imam Mahadi (A.S) ya yi salla bay2an imam (A.S), wannan kuwa zai kasance samar da wani canji da jagorancin soja na musamman, daga karshe za a bude turai da yammacin duniya da dukkan duniya gaba daya[30].

Haka nan wasu ruwayoyi suka zo da cewa; da yawa daga yankunan duniya zasu sallama wa imam (A.S) ba tare da wani yaki ba, kuma yakin duniya zai dauki wata takwas[31] ne kawai, kuma ayoyi da dama kamar “Ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina, kuma addini ya kasance ga Allah kawai” (Anfal: 39). Sun yi nuni da albishir ga nasaran addini da kawar da zalunci da barna, kamar yadda imam Mahadi (A.S) yake fada: “…idan Allah ya yi mana izinin yin magana, sai gaskiya ta bayyana, karya ta gushe…”[32]

Ta yiwu wani ya yi mamakin cewa yaya za a yi mutum daya ya kawo irin wannan canji mai grima a tarihi, shin zai yiwu a samu hakan ta hannun mutum daya?

Tarihi yana bayar da wannan amsa da cewa haka ne, yana ma kawo misalan abubuwan da suka faru wanda aka samu wasu jagororin canji shin na gari suke, ko ba na gari ba: kamar Ibrahim, Musa, Muhammad, a misalan salihai, da kuma Hitlar da Napoliyon a misalan wadanda ba salihai ba. Kuma a wannan zamani na yau muna iya ganin mutum kamar imam Khomain yadda ya canja wa tarihi akalarsa.

Muna iya gani cewa canjin da imam Mahadi (A.S) zai kawo duniya zai fara da kebantattun sahabbansa 313 da kuma taimakon raunanan mutane da talakawansu, sannan ya mamaye dukkan duniya gaba daya ya kuma ci nasarar kafa hukuma ta hanyar juyi mafi girma daga juyin da annabawa har da kakansa Muhammad (S.A.W) ba su iya samar da irinsa ba[33].

Bayan haka, tsawon rayuwa da ya samu, ubangiji ya kara masa[34] da tajriba da basira da abubuwan da suke dole ne a same su domin kawo canji mai girma, don haka ne zai zama ya samu nasara mafi girma a tarihin dan Adam. 

Hada da taimakon Allah da aka shardanta wa al’umma da zai zo musu matukar sun taimaki addinin Allah, sannan kuwa ga alkawarin taimakon aljanu da mala’iku da Allah ya yi masa, a game da wannan al’amari imam Sadik (A.S) yana cewa: “Sai farkon wanda zai sunbanci hannunsa ya kasance Jibrilu ne, sannan sai ya yi masa bai’a, mala’iku ma su yi bai’a, da kuma zababbu daga aljanu sannan sai madaukaka daraja”[35].

A cikin wannan hadisin imam Sadik yana mai amsa wa Mufaddal tambayoyinsa ya yi nuni da cewa; zasu yi gaba da duk wani mai gaba da imam (A.S), sannan zasu bayyana ga mutane su yi mu’amala da su kamar yadda sauran mutane suke mu’amala da junansu, sannan yayin da yake tafiya daga Makka zuwa Kufa da Najaf adadin sahabbansa na mala’iku zasu kai 46 000, aljanu kuwa 6 000. Koda ya ke wata ruwayar ta zo da adadin aljanu da adadin mala’ikun ne, ta hanyar wadannan za a yi masa budi mai yawa[36].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next