ZamaninJuyin Juya Hali



4.Wasumutane masu imani da ikhlasi.

Imam Ali (A.S) yana cewa, wannan bai’ar tana da bangare biyu ne, bangaren hani da na umarni.

Daga cikin bangaren hani shi ne; zai dauk alkawarinsu cewa: “…kada su yi sata, kada su yi zina, kada su zagi wani musulmi…”.

A bangaren umarni kuwa zai umarce su da “…su yarda da dan kadan kuma su yi aiki da kyakkyawa…”.

A wata ruwayar ta zo kamar haka “…ya shardanta wa kansa zai yi tafiya yadda suke yin tafiya, ya sanya tufafi kamar yadda suke sawa…”[54].

A wasu ruwayoyi ya zo cewa; an rubuta “Bai’a ga Allah take” a tutar imam Mahadi (A.S), a wasu ruwayoyin ya zo cewa: a tutarsa an rubuta “Daukaka ga Allah mabuwayi mai girma take kuma ku ji ku bi”[55].

Sannan kuma kishin duniya a matsayin al’umma zai kasance ya karu kuma ya dadu game da juyin imam Mahadi (A.S) domin neman kawo canji da gyara a duniya. Wannan bukatar ta al’umma zata kasance ne daga canjin da ya faru a cikin zukatan al’umma kuma a bisa sunnar Allah ne za a samu canjin rayuwa garesu[56], domin mutane sun riga sun yi mika wuya da biyayya ga kiran imam Mahadi (A.S).

Mutane sun rigaya sun nuna kauna ga imam Mahadi (A.S), kuma dukkaninsu da fari da baki da madaukaka a cikin al’umma da makaskanta daga kowace nahiya da waje zasu taka rawar gani domin kawo nasara ga juyin imam Mahadi (A.S).

Ana iya cewa da farko imam Mahadi yana fuskantar matsala saboda mummunar farfaganda game da kiransa, amma bayan gaskiyar kiransa ta bayyana ga mutane to sai mutane masu tsarkin zuciya da suka hada musulmi da wadanda ba musulmi ba su yi dafifi zuwa ga kiransa.

NaBiyu- Masu Kin Juyin Imam Mahadi

Kamar yadda masu goyon bayan imam Mahadi suka kasu zuwa musulmi da wadanda ba musulmi ba, haka nan masu kin juyinsa suka kasu zuwa musulmi da wadanda ba musulmi ba, wadanda ba musulmi ba sun hada da kafirai, da mushrikai, da masu kin gaskiya wadanda saboda dalili na addini da kuma amfanin kashin kansu da son ransu ne suke kin kiran imam Mahadi (A.S), da kuma sauran ‘yan jari hujja da suke ganin daular imam ta saba wa amfaninsu, da kuma sarakuna da shugabanni azzalumai da za a karbe musu makamansu, da kuma fasikai da suke ganin za a rufe musu wajan fasadinsu. A takaice masu saba wa juyin imam Mahadi (A.S) zasu taru karkashin tutar Sufyani da Dujal da sauran jagororin kafirci ne domin asakala da imam (A.S).

Sabawar wadannan gareshi ba wani abin mamaki ba ne domin ba zasu iya jure wa adalci ba, haka nan wasu musulmi ban da irin wadanda aka ambata zasu yi gaba da shi bisa jahilci wadanda zasu bi shi bayan sun gane gaskiya, amma wasu zasu yi gaba da shi ne saboda karkatattun gurbatattun akidu da suke da su, suna cewa: Hakika wannan ba ya cikin zuriyar Fadima (ko alayen Muhammad), domin da ya kasance daga zuriyarta (ko daga zuriyar alayen Muhammad) da ya tausaya mana[57].

Wadannan jama’a ce da take yada farfagandar cewa yawan kisa ya saba wa tafarkin Annabi (S.A.W), amma idan mun duba zamu ga cewa ayyukansa ba su saba da adalci ba, dukkaninsu domin tsayar da gaskiya ne, don haka duk wani suka a kan hakan ba shi da wani asasi.

Sannan kuma wasu zasu kafirta shi; Imam Khomaini yana cewa: A hukumar imam Mahadi (A.S) adalci zai kafu, amma son rai da ya rage a zukatan wasu mutane shi ne ya zo a wasu ruwayoyi cewa zasu kafrita shi[58]. Kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da cewa wasu daga malamai ma zasu yi musun al’amarinsa[59].

Wasu ruwayoyi sun yi nuni da wannan mas’ala da cewa: “Sai ya tafi Kufa, sai ya fitar da mutum dubu goma sha shida daga cikinta daga masu ibada, masu dauke da makamai, makaranta kur’ani, malaman addini, sun ji wa goshinsu ciwo saboda sujada, sun daure tufafinsu, amma munafunci ya mamaye su, dukkansu suna cewa ya dan Fadima, ka koma mu ba ma bukatar ka, sai ya sanya musu takobi a bayan garin Najaf…”[60].

 [1] Hudu: 86. Naml: 59. Fadir: 32. Maryam:58. Hajj: 75. Ali imran: 33, 42.
[2] Shahid Sayyid Muhammad Bakir Sadar, InkilabuMahadi Wa Fandar Tarjamar Sayyid Ahmad Alamul Huda, Shafi 152 – 163.
[3] Biharul Anwar, Jildi 13, J 15, Shafi 65– 162.
[4] Da jildi 13, j: 53.
[5] Littafin da ya gabata, shafi: 1 – 89,151- 180.
[6] Littafin da ya gabata, shafi: 200 – 317.
[7] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adazzuhur, Shafi: 48 – 57.
[8] Kamar Muhyiddin Bn Arabi, AlfutuhatulMakiyya, J 3, Shafi: 327.
[9] Abu Dawud J 2, Shafi 423, da Suyudi,Alhawi, J 2, Shafi: 102, 129, 150, 152, 174, 341.
[10] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, J 2,Shafi: 865 – 874.
[11] Littafin Da Ya Gabata, J 1, Shafi: 482 –484.
[12] Muhamamd Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur,Shafi: 335 – 339.
[13] Littafin da ya gabata, Shafi: 484.
[14] Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur,Shafi: 335 – 339.
[15] Anwarul Mush’ash’in, J 1, Shafi: 453.
[16] Ruzegare Rahayi, j 1, shafi: 485.
[17] Tarihi ma ba’adaz zuhur, shafi: 443 – 450. Da sauran 1littattafai kamar: Yanabi’ul Mawadda.
[18] Muntakhabul Asar, Shafi 292 – 296 Hadisi Na 1 Zuwa Na 16, Da Shafi: 297 Hadisi Na 1.
[19] Nahajul Balaga, Huduba: 182.
[20] Nahajul Balaga, Huduba: 138.
[21] Allama muahmmad Bakir Majlisi, Biharul Anwar, jildi 13, j 53, shafi: 11.
[22] Allama muahmmad Bakir Majlisi, Biharul Anwar, jildi 13, j 53, shafi: 11.
[23] Allama muahmmad Bakir Majlisi, Biharul Anwar, jildi 13, j 53, shafi: 11.
[24] Muntakhabul Asar, Shafi: 290 – 291,Hadisi 1 - 4.
[25] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 438 – 439.
[26] Abin da ya gabata.
[27] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 861.
[28] Abin da ya gabata.
[29] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, j 2, shafi 1143 – 1156.
[30] Asre Zuhur, Ali Kurani, Tarjeme Abbas Jalali, Shafi: 24 – 30.
[31] Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 558 –602.
[32] Allama Majlisi, Biharul Anwar, j 35,Shafi: 196.
[33] Inkilabe Mahadi Wa Fendarho, Shafi: 179– 181.
[34] Abin da ya gabata.
[35] Biharul Anwar, j 13, j 53, shafi 8 – 11.
[36] Abin da ya gabata.
[37] Ikmaluddin Wa Tamamunni’ima, J 1, Shafi:603.
[38] Kitabul gaiba, shafi: 165.
[39] Safinatul bahar, j 2, shafi: 166.
[40] Hadid: 25.
[41] Imamat wa mahdawiyyat, j 2, shafi: 69.
[42] Abin da ya gabata.
[43] Muntakhabul asar, b 1, f 2, shafi: 147,h 14.
[44] Al’gaiba, Nu’umani, shafi 102.
[45] Abin da ya gabata, shafi: 139.
[46] Tarihu ma ba’adaz zuhur, shafi: 637 –639.
[47] Abin da ya gabata: 649 – 655.
[48] Nahajul balaga, huduba: 138 – 425.
[49] Biharul Anwar, j 52, shafi: 223.
[50] Tarihu ma ba’adaz zuhur, shafi: 404 –416.
[51] Abin da ya gabata.
[52] Abin da ya gabata, shafi: 417 - 420.
[53] Biharul Anwar, j 52, shafi: 125.
[54] Muntakhabul asar, shafi: 469.
[55] Abin da ya gabata 319.
[56] Ra’adi: 11, da Anfali: 53, 54.
[57] Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 603 –619.
[58] Sayyid Ruhul-Lah, Musawi Khomaini,Sahifatun Nur, J 16, Shafi: 105.
[59] Abin da ya gabata, j 19, Shafi: 181.
[60] Dala’ilul Imama, Shafi: 455 – 456.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13