ZamaninJuyin Juya Hali



-Rahabaniyawa ne da dare, zakuna da rana.

-Mafifita mahaya a bayan kasa, ko daga mafifitan mahaya a bayan kasa.

-Runduran fushin Allah kan mabarnata[52].

-Mazaje ne da ba sa baccin dare, suna da wani sauti a sallarsa kamar sautin kudan zuma, suna kwana a tsaye a gefensu, rahabaniyawan dare, zakuna ne da rana[53].

Ruwayoyi masu yawa sun yi nuni da cewa: kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) mabiyansa suna warwatse ne a duniya wadanda suka hada da na sama da na kasa koda kuwa suna kan shimfidar bacci to daga karshe zasu hadu a nan Makka ne a lokaci ayyananne a gefen jagoransu, har ma ana cewa za a samu zuwan mutane 313 Makka ba bisa hanyar al’ada da aka saba ba, a wannan zamani mutanen Makka zasu yi mamakin zuwan wasu mutane baki zuwa garinsu ba bisa yadda suka saba ba.

TunaniDa Kallo Game Da Juyin Mahadi (A.S)

Tunanin mutane da kallonsu game da juyin juya halin duniya na imam Mahadi (A.S) yana zama kala biyu ne:

Nafarko: Tunanin masu goyon baya

Da zarar imam Mahadi (A.S) ya bayyana, muminai na gari da raunanan mutane masu tsarkin zuciya da suka hada musulmi da wadanda ba musulmi ba zasu ba shi goyon baya, kuma bisa wannan kyakkyawan tunani da kallo da suke yi ga wannan al’amari zasu yi wa imam Mahadi (A.S) bai’a daga karshe. Wasu ruwayoyi sun zo cewa: Bayan hudubarsa ta ranar jumma’a wasu bayin Allah da zamu ambace su a nan kasa zasu yi masa bai’a da biyayya gareshi domin samar da hukumar Allah mai adalci a duniya:

1. Jibril(A.S).

2. Sahabbansa masu alaka da shi a boyuwa babba.

3. Sauran mataimaka masu ikhlasi da zasu zo bayan shelanta juyi a Makka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next