ZamaninJuyin Juya Hali



Don haka a bisa wannan mahanga zamu samu cewa musulunci shi ne addinin daidaito, da adalci da karama a fadin duniya, fadin Manzon Allah (S.A.W):

“Shin ba na ba ku labarin Mahadi ba, da za a tashe shi a cikin al’ummata a lokacin sabanin mutane da kaskanci, sai ya cika duniya da adalci da daidaito bayan an cikata da zalunci da danniya, mazauna sama da mazauna kasa zasu yarda da shi, yana raba dukiya da yawa bisa daidaito. Sai wani mutum ya ce: menene daidaito? Sai ya ce: Daidaita wa tsakanin mutane, zai kuma cike zukantan mutane da wadata, ya yalwace su da adalcinsa[43]”.

Ana iya cewa musulunci duk da ya kasance wani abu ne dadadde amma kuma zai kasance sabo, duba fadin imam Sadik (A.S): Daga Abu basir daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: …kamar ina ganin sa a tsakanin rukuni da Makamu Ibrahim yana karbar bai’ar mutane a kan sabon littafin da al’amarinsa mai tsanani ne a kan larabawa[44].

Imam Bakir (A.S) yana cewa: Na rantse da Allah kamar ina gannin sa tsakanin rukuni da makamu Ibrahim yana karbar bai’ar mutane a kan sabon al’amari da sabon littafin, da sabon iko daga sama[45].

Idan mun duba zamu ga abubuwa biyar da wadannan ruwayoyi da wasunsu suka kunsa su ne:

Al’amari sabo

Sunna sabuwa

Hukunci sabo

Karfin iko sabo

Kira sabo



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next