ZamaninJuyin Juya Hali



Wani abin da zai taimaka masa shi ne sanya tsoro a zukatan makiyansa da Allah zai yi: Shaikh Saduk ya rawaito a littafin kamaluddin cewa: Daga Muhammad dan Muslim assakafi yana karbowa daga imam Bakir (A.S) ya ce: “Mai tsayawa daga cikinmu abin taimakawa ne da firgitarwa, abin karfafa ne da nasara”[37].

Daga Abu Basir, ya ce: Abu Abdullah ya ce: …yana tafiya firgitarwa tana rigonsa da wata daya, a bayanta wata daya, a damanta wata daya, a hagunta wata daya…”[38].

Don haka ana iya cewa, duk da makiyan imam Mahadi (A.S) suna da makami amma makamin zahiri ba shi ne sirrin cin nasara ba; Sannan kuma bayan makamin zahiri ana bukatar makamin badini domin cin nasara, don haka ne ma muka ga saudayawa an samu mutane masu rauni sun ci galaba a kan masu karfin makamai, wannan misali muna iya ganin sa a fili a yakin Amurka da Biyatnam.

Wani babban misalin shi ne cin nasarar mutanen Aljeriya a kan Faransa, da kuma nasarar da imam Khomaini ya samu a kan sarki Sha, wanda yake da makamai da kariyar Amurka da Ingila. Ta kowane hali dai cin nasarar imam Mahadi (A.S) wani abu ne wanda ba shi da makawa kamar yadda ya zo a ruwayoyi daga ma’asumai, kuma babu wata shubuha a kan hakan.

Na Biyar- Fikirar Juyin Duniya Na Imam Mahadi

Ba kokwanto cewa duk wani juyi a duniya yana dauke da wata fikira da yake son isarwa da yadawa, amma fikirar juyin imam Mahadi (A.S) zata kasance musulunci ne, wannan fikira zata zama sanadiyyar rushewar zalunci ta hanyar nuna adalci da yanayin walwalar jin dadin al’umma da ake hankoron kaiwa gareshi.

Tun da musuluncin da Mahadi (A.S) zai nuna wa duniya shi ne mafi kosar da bukatun dan Adam, saboda haka ne zai kasance dalilin motsi mai girma domin rushe zalunci da sadaukarwa da yakar azzalumai.

Mafi girman asasin da za a yi kira zuwa gareshi shi ne tsayar da adalci, al’amarin da mafi yawan ruwayoyin Shi'a da Sunna da zuka zo suke nuni zuwa gareshi, kuma ta hanyar fassara kur’ani da tafsiri mai inganci da sahihin tawili wannan zai kai ga rushewar sauran fikirorin da sauran addinai suke dauke da su.

Wannan fikirar ta imam (A.S) tana kunshe da taken cewa: “Da adalci ne sammai da kasa suka tsayu”[39]. Don haka ne samar da adalci ya kasance mafi girman asasin addinin ubangiji kamar yaddda koyarwar kur’ani mai girma ta nuna, aikin annabawa shi ne tsayar da adalci a cikin al’umma da taimakon mutane garesu[40].

Koda yake annabawa da suka gabata sun tsayar da adalci amma bai samu yaduwa ko’ina a sasannin duniya ba, sannan ya bayyana cewa: juyin imam Mahadi (A.S) wani juyi ne na addini da yake a fili.

A wannan juyin ana kore duk wani tunani na rashin imani da addini, kuma addini ba kawai yana takaita da daidaikun mutane ba ne a al’amarinsu na kashin kansu, har ma yana kasancewa wani abu ne na al’umma da zamantakewa da ya shafi al’amarin mutane a rayuwarsu ta al’umma a tare gaba daya



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next