ZamaninJuyin Juya Hali



ZamaninJuyin Juya Hali

Na Daya- Share Fagen Fikirar Hakikar Juyin Adalci

Hakika kowane juyi yana bukatar gabatarwa, da sharudda na fikira da tunani, muna iya sanya rashin yardar mutane a dukkan duniya daga zaluncin da ya yadu a cikinta na azzaluman dauloli da kuma neman al’umma ga samar da adalci da sulhu a duniya ta wani bangaren a matsayin abubuwan na dole masu share fage domin samuwar juyin juya halin duniya na imam Mahadi (A.S).

Abin da zai wakana a duniya na faruwar zaluncin azzalumai da yawan nuna rashin yarda ta hanyar tawaye da muzaharori da yajin aiki, da lalacewar al’amura da zai kai ga yanke kauna har sai wasu sun yi kokwanton samuwar Mahadi (A.S) da dawowar adalci duniya ta yadda yanayi zai zama ba zai juru ba, har sai ya kasance dan Adam ba shi da wani fata sai samar da da mai tseratar wa daga wajen ubangiji madaukaki wanda zai fitar da duniya daga wannan kangi da ta fada cikinsa. Wannan duk abubuwa ne da suke iya share fagen bayyanarsa (A.S) kuma zamanin neman dawowar adalci da wannan zai fara a duniya.

Amma mu sani neman adalci kawai ba ya iya sanya bayyanarsa, don haka dole ne ya zama akwai wani sharadi da zai cika wanda yake nufin samuwar wani tunani na addini ko mazhaba mai dauke da wannan fikira game da karshen zamani da kawo adalci a duniya gaba dayanta.

Wannan tunanin na neman tattaunawar kawo adalci shi ne abin da zai shagaltar da kwakwalwar mutumin karshen zamani musamman idan aka yi duba zuwa ga kishirwar adalci. Tattaunawar neman adalci da sannu zata karya tattaunawar yin zalunci a kan kasashe kuma zata raunatar da fikirar da ta doru a kai, kuma yawan masu neman adalci a cikin kowace irin al’umma zai samu karuwar karbuwa.

Wannan tunani na tattaunawa neman adalci da sannu zai mamaye tunanin mutane ya kuma share wa dan Adam hanyar yunkurin kaiwa ga samun juyin cikin rayinsa domin samar da adalci a cikin rayuwar dan Adam.

Wannan guguwar neman zata kada tare da neman yin adalci a duniya gaba daya daga gabas ta tsakiya, yayin da neman samar da adalci ya rigaya wutarsa ta huru a dukkanin sasannin duniya, dan Adam ya kasance da gaske yake wajen neman tabbatar adalci a duniya da izinin Allah.

Kuma jagoran juyin duniya zai samu karbuwa saboda masaniyarsa game da dukkan addinan Allah, kuma zai samu kaiwa zuwa ga cin nasara ta hanyar nuna musulunci a matsayin asalin addinan halittar Allah mai tsarkin ruhi.

Zai fuskanci masu zalunci domin tsayar da adalci a bayan kasa gaba daya, rundunar imam Mahadi dan Hasan Askari (A.S) zasu daga tutar neman adalci domin kaiwa ga tabbatar alkawarin Allah da ya zo a cikin kur’ani mai girma:

“Hakika mun aiko manzanninmu da dalilai kuma mun saukar da littafi da ma’auni tare da su domin mutane su tsayu da adalci, kuma mun saukar da karfe da yake da tsanani mai karfi a cikinsa da amfani ga mutane, kuma domin Allah ya san wanene zai taimake shi da manzanninsa a fake, hakika Allah mai karfi ne mabuwayi. Hadid: 25.

Juyin juya halin imam Mahadi (A.S) bai takaita da wani bangare ba, ya shafi dukkan bangarorin rayuwa da ya hada kyautata rayuwar mutane na halin tattalin arziki, da kawar da talauci, da yalwata dukiya da arziki, da kawo aminci a bayan kasa gaba daya, da warwarar matsalar al’amuran zamantakewar al’umma, da juyin neman adalci, da tabbatar da dukkan bangarorin siyasa da karfin soja, da al’adu, da wayewa, da sauaransu.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next