Tambayoyi Da Amsoshin Akida



9.      Balaga

10.  Takawa

Duk wanda ba mujtahidi ba ne, kuma ba mai yin ihtiyadi ba, kuma bai yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda ba, to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, koda kuwa ya yi salla, ya yi azumi, ya yi ibada duk tsawon rayuwarsa, sai dai idan aikinsa ya dace da ra’ayin wanda yake yi wa koyi kuma ya yi sa’ar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah (S.W.T).[5]


Wanene Ubangiji Madaukaki?

Ubangijin shi ne; mai samarwa ga dukkan ababan halitta gaba daya, wanda yake guda daya ne makadaici, babu wani abu kamarsa, magabaci ne, bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, babu maikama da shi, ba shi da kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi. Gannai ba sa riskarsa Shi kuwa yana riskar gannai.

Duk wanda ya kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, haka nan dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (A.S).[6]


Menene Hakikanin Tauhidi?

Tauhidi shi ne kadaita Allah ta kowace fuska kamar kadaita shi a zatinsa, da cewar shi kadai ne a zatinsa kuma da kadaita shi a siffofi da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa, da kuma kasancewar ba mai hukunci sai shi, kuma ba wanda yake shar'antawa sai shi, kuma ba wani mai tafiyar da al'amuran bayi sai shi.

Wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada shi da wani abu a nau’o’in ibada. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da shi a ibada to shi mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu[7].

Menene Siffofin Ubangiji (S.W.T)?

Siffofin Allah (S.W.T) sun kasu kamar haka; Siffofinsa tabbatattu na kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinsa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinsa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu biyuntaka a siffofinsa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.

Kashi na biyu su ne; Tabbatattun siffofi na idafa[8], kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.

Kashi na uku su ne; Siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai tawaya da nakasa, kamar jahilci, da gajiyawa, da mutuwa, da kurumta, da talauci, da kasancewarsa ba wajibin samuwa ba, wato ya zama mai yiwuwar samuwa[9], da sauran siffofi na tawaya da rashin kamala.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next