Tambayoyi Da Amsoshin Akida1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi[26]: “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shiâ€. “Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni. 2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan[27]: Abu Ja’afar (AS) “Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba? Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu. Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan. Sa’id: To halaka ke nan. Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna. 3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Alkinani[28]: Alkinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
|