Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Kuma ya kalubalance su da su kawo sura goma suka kasa, yayin da muka ga sun gajiya sai muka ga sun koma fada da shi da takobi maimakon harshe, sai muka san cewa lallai Kur’ani wani abu ne na mu’jiza da ya zo daga Muhammad dan Abdullahi hade da da’awar manzanci, sai muka san cewa ya zo ne da gaskiya kuma ya gasgata shi[36].

 

Menene Hakikanin Ismar[37] Annabawa?

Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu kuma da kubuta daga mantuwa. kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukkan abin da yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane, ko kuma kyalkyala dariya da sauti mai girma, da dukkan aikin da ake munana yin sa a tsakanin mutane.

Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi shi ne: Da ya halatta ga Annabi ya aikata sabo, ko kuma ya yi kuskure, ko ya yi mantuwa, ko wani abu makamancin wannan ya auku daga gare shi, da sai ya zamanto imma dai ya wajaba a yi masa biyayya a aikin da ya yi na sabo ko kuskure, ko kuwa bai wajaba ba. Idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, kai mun wajabta ne ma, wannan kuwa abu ne batacce na larurin Addini da na hankali. Idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka, to kuwa wannan ya kore Annabcin da babu makawa tana tare da wajabcin biyayya har abada.

Ta kowane hali dai aiki ko zance ya zo daga gareshi da ya zama muna tunanin sabo ne ko kuskure, sai ya zama ba wajibi ba ne a bi shi a cikin kowane abu, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan, sai Annabin ya zama kamar sauran mutane da maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da’iman, kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba, babu kuma nutsuwar zuciya da maganganunsa da ayyukansa baki daya.

Menene Hakikanin Siffofin Annabi?

Bayan Isma wacce take daya daga siffofin annabawa, haka nan dole ne annabi ya zamanto mai siffantuwa da mafi kamalar siffofin dabi’u da hankali wadanda mafifitan su, su ne ilimi, da jarumtaka, da iya tafiyar da al’amuran mutane, da shugabanci, da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba, da bai inganta ba ya zamanto yana da shugabanci a kan dukkan halittu baki daya, ko ya zamanto yana da karfin tafiyar da al’amuran duniya dukkaninta ba.

Haka nan wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya, wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi’u kafin aiko shi saboda zukata su nutsu da shi, rayuka kuma su karkata zuwa gareshi, kuma domin ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.


Menene Hakikanin Annabawa Da Littattafansu?

Hakika dukkanin annabawa masu gaskiya ne, kuma ma’asumai ne ga barin dukkan tawaya ta aiki, da dabi’a, da ta halitta da takan iya rusa hadafin aiko su, kuma tsarkaka ne. Musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu.

Wadanda aka san sunayensu da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Kur’ani ya ambace su a sarari, ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya, kuma ya karyata Annabcin annabinmu a kebance.

Haka nan ya wajaba a yi Imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen wadanda aka canza su daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S), saboda wasan da ma’abota son rai da kwadayi suka yi da su, wadanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagaggu ne da aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S).


Menene Hakikanin Musulunci?

Musulunci shi ne addini yardajje a wajan Allah, kuma Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar Dan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da Dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar Musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za ta zo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin Musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next