Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.

Fannin likitanci bai musanta tsawon rayuwa fiye da dabi’a ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari, idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Kur’ani ya ba da Iabari game da shi, to sun yi hannun riga da musulunci.

Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhalin yana da’awar imani da kur’ani.

Yana da kyau mu sani cewa; sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a, kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa, kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa”. Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S), wanda yake mai shiryarwa da aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi[52].

Mecece Ranar Tashin Kiyama?

Ranar tashin kiyama rana ce da Ubangiji zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawarinta, sai ya saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo, wannan al’amari ne da baki dayansa da abin da ya tattaro na daga sauki, abu ne wanda dukkan shari’o’in da aka saukar daga sama da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, kuma babu wata madogara ga musulmi sai dai ya yi imani da akidar Kur’ani mai girma wacce Annabinmu mai girma ya zo da ita. Domin duk wanda ya yi imani da Allah imani yankakke, ya kuma yi imani da Muhammad manzo ne daga gare shi, wanda ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya, to babu makawa ya yi imani da abin da Kur’ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni’ima, da wuta da kuna. Kuma Kur’ani ya bayyana haka a sarari, kuma ya yi nuni da shi a cikin abin da ya kai kusan ayoyi dubu.

Idan har shakku ya samu wani game da wannan, ba don komai ba ne sai domin yana shakku game da ma’abocin sakon, ko kuma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, ba komai ba ne sai shakkun da yake bujuro masa game da asalin addinai dukkaninsu, da kuma ingancin shari’o’i gaba dayansu.

Menene Hakikanin Tayar Da Jikin Halittu?

Tayar da jiki wani al’amari ne da yake larura daga laruran addinin musulunci, Kur’ani mai girma ya yi ishara game da shi: “Shin mutum yana tsammanin ba zamu tattara kasusuwansa ba ne. A’aha, Lalle mu masu iko a kan mu daidaita yatsunsa ne”. Surau Alkiyama: 3.

Da fadinsa: “Idan ka yi al’ajabi to abin al’ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka mutu muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa”. Ra’ad: 5.

Da fadinsa: “Shin mun gajiya ne da halittar farko, sai dai su suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta”. Surar Kaf: 14.

Tayar da jikkuna ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa, da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da jikkuna fiye da abin da Kur’ani ya ambata, ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi, da Siradi, da Auna ayyuka, da Aljana, da Wuta, da Sakamako, da Ukuba, daidai gwargwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur’ani mai girma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next