Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Amma sai ga masu shisshigi ga karfin Allah da ikonsa suna taurin kai da kin rusunawa gaban wannan karfi na Allah suna jahiltar kawukansu, suna mamakin tashin kabari da tashin kiyama, suna masu fadar: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Madaukaki mai karfi yana yi masu bayani da cewa: “Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsa, ya ce: Wanene zai rayar da kasusuwa alhalin suna masu rididdigewa”. Yasin: 77-78. Kur’ani yana amsa wa irin wadannan gafalallu da cewa: “Ka ce wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. Yasin: 79.

Kuma ya ce da shi: Ba ka da wata mafita sai mika wuya ga mahaliccinka mai hikima da iko, kana mai sallama wa gareshi, kuma abin da ya kamata gareka shi ne; shagaltuwa da tsarkake kanka daga daudar sabo, da siffantuwa da siffofin kamala domin samun tsira a ranar da take: “Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta, kuma ba a karbar fansa daga gareta, kuma ba a taimakon su”. Bakara: 48.

Godiya Ta Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai


[1] - Surar Lukman: 12.

[2] - Akidoji imamiyya, Babin Imaninmu game da Sani da Nazari a kan samuwar Allah.

[3] - Shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta canzawa ko sakewa da sakewa zamani da kuma halaye.

[4] - Ihtiyadi shi ne bin fatawar malamai da aiki da mafi nutsuwar zance daga cikin fatawowinsu.

[5] - Akidojin imamiyya Babin Imaninmu game da koyi da wani a rassan al'amuran addini.

[6] - Akidojin imamiyya, Babin imaninmu game da Ubangiji madaukaki.

[7] - Akidojin imamiyya, Babin imaninmu game da Ubangiji madaukaki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next