Tambayoyi Da Amsoshin Akida Shin Akwai Koyi A Rassan Al’amuran Addini?
Wajibi ne a cikin rassan hukunce-hukucen addini idan ba laruran Addini ne ba ne kamar wajabcin salla, da zakka, da azumi, da hajji, mukallafi ya yi dayan al’amura uku a cikinsu: - Ko ya yi ijtihadi[3] ya yi bincike a kan hukunce-hukunce daga fatawoyin mujtahidai idan yana cikin masu iya yin hakan, ko kuma ya zama mai ihtiyadi idan zai iya yin ihtiyadi[4], Ko kuma ya yi koyi da mujtahidin da ya cika sharrudda kamar haka; 1. Hankali 2. Adalci 3. Kamewa 4. Kiyayewa 5. Sabawa son rai 6. Bin umarnin Allah 7. Dan halal 8. Ilimin ijtihadi
|