JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).Wajibi ne mai binciken tarihin musulunci ya yi tambaya kan musabbabin yaduwar wilaya ga Ahlulbaiti (a.s). Shin yana yiyuwa hakan ta tabbata ba tare da samuwar wani aiki mai yawa da tsari, wanda aka auna shi, wanda kuma hadadde ne wajen tafarki da manufa ba? Amsa a’a, bisa dabi’a wannan ba zai yiwu ba. Gagarumar farfagandar da mulkin Umayyawa suka dana ta hanyar daruruwan alkalai da hakimai da masu huduba ba za ta rushe kuma ta ci tura ba idan ba wata tsararrar farfaganda mai hamayya da waccar, wacce wani tsari hadadde, daidaitacce, boyayye ya yunkura da ita ba. Dab da mutuwar Mu’awiya aikace-aikacen wanna shirin Alawiyyawan ya ci gaba, saurinsa kuma ya karu. Lamarin ya kai ga hakimin Madina ya rubuta wa Mu’awiya abin da ya kunshi wannan: “Bayan haka, Umar ibn Usman (dan leken asirin hakimin Madina wanda ya sa ido kan Imam Hussain (a.s)) ya ba mu labarni cewa wadansu mazaje daga Irak da sashen manyan mutanen Hijaz suna yawan zuwa wajen Hussain Ibn Ali, suna kuma tattauna batun daga tutar tawaye …….ku rubuto mana ra’ayin ku.â€[21] Bayan waki’ar Karbala da shahahar Imam Hussain (a.s) aikin tsare-tsare na shi’a a Iraki ya karu sakamakon girgizar da ta sami zukatansu saboda kisan Imam Hussain (a.s) inda wannan babban laifi wanda ya kwace musu damar shiga ayarin Hussain da mutanen gidansa a Karbala ya zo musu ba zata. Wannan motsawa tasu tana kewaye da jin zafi da tabewa da takaici. Dabari ya ce : mutanen basu rabu da tara kayan yaki da shirya masa da kiran jama’ar shi’a da ma waninsu, a asirce, kan daukar fansar jinin Hussain ba. Mutane sun amsa kiransu jama’a na bin jama’a, birni na bin birni, ba su rabu da haka ba har Yazid ibn Mu’awiya ya mutu.[22] Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:- “Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a mai tsari, ra’ayoyin addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tararraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji. Jama’ar “Tawwabun†ita ce farkon mai bayyana dukkan wanna. Bincike kan al’amuran da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihi kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar fusata da sukar Banu Umayya ta fi tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace haraka mai rinin shi’a . Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yiamfani da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti(a.s) Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan cewa bayan shahadar Imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata babbar harakar shi’a. Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a,watau mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa. Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su
|