JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su

  suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a, wanda ta jefa tsoro da firgici  a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya gamu da mai da martani mai tsanani.

A takaice, a karnin farko da na biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadi na tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda  dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alawiyyawa na musulunci. Wannan alaka ita ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.

Bisa hakika jama’ar shi’a  suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya.  Wannan shi ne takaitaccen  bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman  Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da  ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba! Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba  tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba.

Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.

Daga cikin kalmomi masu zurfafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu  talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa” da “wakili” da “ma’abocin sirri” wadannan kalmomi ne da ake  kiran wasu sahabban imami da su. Alal misali mashahurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s) cewa :- “ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa” a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsa”, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:-  “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsa”. A cikin littafin “Rijalul Kashshi” ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirri”. A cikin littafan hadisi ana ruwaito kalmar “wakili” daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais. Ko wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar Ko ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyau kan wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamai (a.s) suke gudanarwa,  akwai wani rayayyen shiri na boye.

  Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.


[1] Biharul Anwar 47: 13.

[2] Rijal na Alkashshi :158.

[3] Usulu kafi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next