JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Wannan abu ne wanda ba za a iya gano shi ba. Abin da hankali zai kama shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan ta. Wannan  ita ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar  rashin  gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin  idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to  ya zama wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu da rabi, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).

Me ake nufi da tsari?  Ba fa tsari a nan yana nufin  wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba. Ba kuma samuwar wasu dakaru tanadaddu masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba. Babu wannan, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayya kan wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.

Wannan  jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Ali na halifanci yana hada ta. Ta kan bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin tada abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawa kan abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude. Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.

Wadanda suka shahara daga cikinsu akwai Salman da Ammar da Abu Zarri da Ubayy ibn Ka’ab da Mikdad, da  Huzaifa da sauransu, daga manyan sahabbai.

Muna da shaidun tarihi masu tabbatar da cewa wadannan suna yada tunaninsu kan al’amarin imamancin Ali (a.s) cikin mutane  tare da hikima. Wannan aiki nasu ya zama gabatarwa ga dafifin da mutane suka yi kan Imam Ali (a.s) da kafa hukumarsa.

Bayan Imam Ali (a.s) ya karbi ragamar mulki shekara ta talatin da biyar bayan hijira mutane iri biyu suke tare da shi. Na farko sun san Imam da matsayinsa, sun fahimci ma’anar imamancin sun kuma gaskata shi. Wadannan su ne shi’arsa wadanda suka yi tarbiyya a gabansa ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wadansu. Kashi na biyu ya kunshi jama’a baki daya wadanda suka rayu cikin yanayin tarbiyyar Imam da tafarkinsa amma basu da alaka ta tunani ko ta ruhi  da jama’ar da Imam ya yi wa tarbiyya ta musamman.

Saboda haka ne za ka sami mabiya Imam iri biyu ne na mutane, tsakaninsu da fifiko mai yawa. Kashi guda ya hada da Ammar da Malik Ashtar da Hujr ibn Adiy da Sahl ibn Hunaif da Kais ibn Sa’ad da tamkarsu. Daya kashin kuwa ya hada da Abu Musa AlAsh’ari da Ziyad ibn Abih da ire-irensu.

Bayan sulhin Imam Hassan (a.s) muhimmin matakin da Imam ya dauka shi ne yada tunanin mazhabin Ahlulbaiti da daidaita tsakanin masu wilaya da wannan tunanin, tun da an sami faragar motsawa mafi yalwa sabili da danniyar mulkin Umayyawa. Da’iman haka al’amarin yake, danniya tana kawo hadin kan wadanda ake dannewa ya sa su sajewa da kafuwa a maimakon watsewa da rarraba. Dabarun  Imam Hassan sun fuskanci tara karfi mai wilaya dan asali waje guda da kare shi daga rabkar tsarin Umayyawa, da kuma yada tunanin musulunci dan asali a tsakanin wata takaitacciyar kungiya, sai dai an zurfafa koyar da su wannan tunanin. Sauran ayyuka sun hada da neman masu  shigowa safun wilaya da dakon damar da ta dace da yin tawaye wa tsarin zalunci: da yin bindiga da ginshikansa da kuma aza hukuma Alawiyya a gubinsa. Wannan dabarar aiki ita ta bar Imam Hassan (a.s) da zabi daya kadai, wanda shi ne sulhu.

Wannan shi ya sa muke ganin wani gungun ‘yan shi’a karkashin jagorancin Musayyib ibn Najiyya da Sulaiman ibn Sard Alkhuza’i, ya tafo gurin Imam Hassan (a.s) a Madina bayan sulhu, yayin da ya dauki birnin ya zama cibiyar aikinsa na tunani da siyasa bayan dawowarsa daga Kufa. Wadannan mutane suna gabatarwa Imam da shawarar sabonta karfinsu da tsare-tsarensu na soji da mamayar Kufa da yin tafo-mu-gama da rundunar Sham. Imam ya yi kiran wadannan mutane biyu daga cikin gungun,  ya kebance da su, ya kuma tattauna da su kan abin da ba mu san me ya kunsa ba. Mutanen nan biyu sun fito a karshen wannan tattaunawa tare da cikakken gamsuwa da rashin alfanun daukar wannan mataki. Yayin da wadannan biyun suka koma ga wadanda suka zo tare da su sai suka fahimtar da su a takaice cewa an yi watsi da batun tawaye ta hanyar daukar makami, kuma dole  ne a koma Kufa domin a sake sabon aiki a can.[17]

Wannan muhimmin al’amari ya kunshi ma’anoni masu girma wadanda  suka sa sashen malaman tarihi na wannan zamani daukar wancan zama a matsayin tushen da aka kafa tsare-tsaren shi’a a kansa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next