JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).A maganarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s) yana kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi†kan cewa a ra’ayin musulunci basu cancantar shugabanci. Ana iya ganin wannan sigar suka kan tsari mai mulki a sarari da fayyacewa a darusansa na fikihu. An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu, kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsaâ€[13] Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki wata hanya ba ta Allah ba. Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[14] A koyarwar imamai ( a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawa kan wajibcin gwama jagorancin siyasa da tunani da manufa (aidiyolojiyya). A wata riwaya daga Imam Ali ibn Musa Al Rida (a.s) daga kakansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Makami a gare mu tamkar akwati ne ga Bani Isra’ila, duk inda akwati ya juya, sai mulki ya juya, (ka yi tunani da kyau kan ma’ana irin ta alama (ramzu) da ke cikin maganar) duk kuwa inda makami ya juya a cikinmu ilmi can zai juya. A wata riwayar kuma duk inda makami ya juya a cikinmu, to can al’amarin (hukuncin) yake. [15] Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:- Shin makamin yana rabuwa da ilmi? Imam ya ce:- A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba, cikakkiyar sabawa, da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannan yana tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imam yake baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa. Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawa na farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, sun kasance suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya kan da yawa daga hanyoyi da sako-sako na kiran. Sun riski rawar da hari da fama da wannan aikin fikihu da hadisi da tafsiri ke takawa fiye da magabatansu, Umayyawa. Hala wannan dalilin shi ya sanya Mansur, saboda tinkarar Imam Sadik (a.s) ya hana shi zama a halakar koyarwa na wani lokaci da hana mutane zuwa gare shi. Har Mufaddal ibn Umar yana cewa:- “ Hakika Mansur ya daura aniyar kashe Abu Abdillah ba ma sau daya ba, ko yaushe ya aika a kira shi domin ya kashe shi, idan ya dube shi sai haibar Imam ta rufe shi kana ya bar shi, sai dai fa ya hana mutane zuwa gare shi, ya kuma hana shi zama saboda mutane, ya bincike shi bincike mai tsanani, har al’amarin ya kai ga cewa waninsu zai bukaci samun haske a wata mas’alar addini kan batun aure ko shika ko wani abin daban, gashi basu da sanin ta, kuma basu iya isa gare shi. Sai mutum ya kaurace wa iyalinsa. Wannan abu ya kuntata wa shi’arsa ya kuma yi musu tsananinâ€[16] 3. Kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa. Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadi wanda kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na Ali (a.s) da bayyana sha’anin imamanci a kan sahihiyar ma’anarsa. Wannan shirin sadarwa ya yi yunkurin tabbatar da aikin yada ma’anonin imamanci. Wannan yunkuri ya yi alfanu saboda irin tasirinsa a sassan duniyar musulunci masu nisa masamman a Irak da Kurasan. A nan za mu yi ishara ga kadan daga wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamai yana daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari, a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yi yu mu sami bayanin wannan al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.
|