JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori. Daga cikin kalmomi masu zurfafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa†da “wakili†da “ma’abocin sirri†wadannan kalmomi ne da ake kiran wasu sahabban imami da su. Alal misali mashahurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s) cewa :- “ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa†a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsaâ€, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:- “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsaâ€. A cikin littafin “Rijalul Kashshi†ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirriâ€. A cikin littafan hadisi ana ruwaito kalmar “wakili†daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais. Ko wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar Ko ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyau kan wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamai (a.s) suke gudanarwa, akwai wani rayayyen shiri na boye. Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria. |
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 | next |