JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a) 3. kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa. Hanyar da bahasinmu zai dauka ita ce yin bincike kan kowani daya daga wadannan alamomi sannan daga karshe mu sanya wani jadawalin ayyukan Imam (a.s) Duk wannan zai kasance da salon masu tarihi ba na masu hadisi ba, gwargwadon iyawarmu. 1. Bayyana sha’anin imamanci da kuma yin kira zuwa gare shi. Wannan maudu’i yana daukar masayin mafi bayyanan alamomin kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) tun shekarun farko bayan kaurar Annabin rahama (s.a.w.a). Mas’alar tabbatar da imamancin Ahlulbaiti ita ce al’amari na kan gaba wajen kira a dukkan zamunnan imamanci. Muna iya ganin wannan mas’alar a yunkurin Imam Hussain ibn Ali (a.s) da kuma yunkurin ‘ya‘yan imaman Ahlulbaiti kamar Zaid ibn Ali. Kirar Imam Sadik ita ma ba ta fita daga wanna fagen ba. Kafin mu bijiro da hujjoji kan wannan maudu’i ya zama wajibi tukun mu fara da bayanin ma’anar (imama) ‘imamanci’ a tunanin musulunci. Kuma mene ne kira zuwa ga imamanci? Kalmar imamanci a asalinta tana nufin jagoranci sake ba kaidi. A tunanin musulunci kuwa galibi ana amfani da ita ne a kebance. Wannan wurin kuwa shi ne jagoranci a sha’anin halin zaman jama’a walau wajen tsarin tunani ne ko kuwa tsarin siyasa. Kalmomin da aka tsago daga ita kalmar ‘imama’kamar su ‘imam’ da ‘a’imma,’ duk inda suke a cikin Alkur’ani abin da ake nufi da su shi ne kebantaciyar ma’anarsu watau jagorancin al’umma. A wadansu wurare abin da ake nufi da ita shi ne jagorancin tunani a wadansu kuwa jagorancin siyasa ko kuma biyun gaba daya. Bayan kaurar Ma’aiki da bayyanar rarrabuwar salon tunani da siyasa tsakanin jama’ar musulmi, kalmar imamanci, da imama, ta dauki wani kebantaccen masayi, saboda mas’alar jagorancin siyasa ita ce jigon sassabawar musulmi. Da farko, kalmar tana da manufar siyasa fiye da kowace manufa wacce ba ta siyasa ba. Daga bisani wadansu ma’anonin sun riske ta sannu a hankali, har aka wayi gari a karni na biyu mas’alar ‘imama’ ta zamo mas’ala mafi muhimmanci wajen makarantan ilmul kalam masu baiyana ra’ayoyinsu kan sha’anin sharuddan imam da sifofinsa, watau sharuddan mai hukunci a al’ummnar musulunci; wannan kuwa shi ne ma’anar imamanci a siyasance. A makarantar Ahlulbaiti, wacce mabiyanta suke ganin kansu a matsayin ma’abota ra’ayin tunanin musulunci mafi tsabta, ita ma tana daukar kalmar imamanci da wannan ma’ana. Nazariyyar wannan makaranta kan sha’anin imamanci, a takaice, ita ce:- Imami ko kuma shugaban siyasa a al’ummar musulunci dole ne ya zama abin nadawa daga Allah ta hanyar sanarwa daga Annabi. Dole ne ya zama jagora a tsarin tunani, mai fasssarar Alkur’ani , masanin dukkan mas’alolin addini masu zurfi da rikitarwa (daka’ik)da kuma alamu irin na ramzi a cikin addini. Wajibi ne ya zama ma’asumi wanda aka kubutar daga duk wani aibi na halitta ko dabi’u ko aibin da taliki yake janyo wa kansa. Wajibi ne ya zama ya fito ne daga tsatso mai tsarki da tsabta.
|