Mutahhari Da Gwagwarmaya



5-Musulmi su anfana da ilumman masana'antu da kimiyya da fasahar Turawan Yamma amma da kiyaye ruhin Musulunci da kore irin tunanin Turawan game da duniya.

6-Musulmi su siffantu da ruhin jihadi, su dawo da ruhin nan na su na izza da daukaka; ta yadda ba za su karbi zalunci, kaskanci da danniya ba.

Mutum Tara Yake:

Shahid ya bayyana cewa a iyakla saninsa Sayyid Jamaluddin Afgani bai bayyana ra'ayinsa game da tsarin iyali da tsarin karatuttukan Musulunci ba. Don haka, in ji Shahid :

Ba mu san yadda Sayyid Jamaluddin ke kallon wadancan tsare-tsare da ma'aunin Musulunci ba".

Haka nan Allama ya bayyana cewa Sayyid Jamaluddin bai waiwaiyi falsafar siyasar Musulunci, yanayinta da hange-hangenta ba, duk kuwa da ya kasance mai matukar yakar 'yan mulkin mallaka da 'yan kama-karya. Wata kila, Allama ya ci gaba da cewa, saboda nutsuwarsa cikin yaki da mulkin-mallaka da kama-karya ne ba su ba shi daman yin haka ba.[10] Wata kila ya yi imani ne da cewa fada da mulkin-mallaka da kama-karya shi ne mataki na farko a gwagwarmayar Musulunci, da cewa matukar Musulmi sun yi nasara a matakin farko, to lokacin ne za su san abin da za su yi a mataki na biyu. Ta iya yiwuwa kuma, in ji Allama, mu dauki hakan a matsayin nakasa a cikin ayyukan Sayyid Jamaluddin.

Sheikh Mugammad Abduhu

Wani mutum da Ustaz al-Shahid ya kalla daga cikin 'yan gwagwarmaya a wannan zamanin, kuma wanda ra'ayin Shahid game da shi ke iya ba mu hoton tunaninsa game da gwagwarmayar Musulunci a karnonin baya-bayan nan, shi ne Sheikh Muhammad Abduhu. Ya kasance almajiri kuma abokin Sayyid Jamaluddin Afagani. Sheikh Muhammad Abduhu ya yi imani da cewa duk abin da ke gare shi a wannan tafarki daga Sayyid Jamaluddin ne.

Allama al-Shahid ya bayyana cewa bayan Sheikh Muhammad Abduhu ya rabu da Sayyid Jamaluddin ya koma Masar, abin da ya shagalta tunanisa a lokacin shi ne al'amarin Musulunci da Bukatun Zamani. Ya kasance yana tunani kan hanyar da za ta hada Musulunci da ilimin zamani da ci-gaba a tsakanin al'ummar Masar. Wannan kuwa saboda ganin yadda wasu malaman addini suka daskare ne.

Sheikh Muhammad Abduhu, sabanin Sayyid Jamaluddin, ya kasance yana jin wannan nauyi ne a matsayin malamain addini; don haka ya kasance yana neman hanyar da zata kubuta daga gazawa da wuce-gona-da-iri a wannan fagen. Wannan ya sa Sheikh Muhammad Abduhu ya bijiro da wasu al'amura da Sayyid Jamaluddin bai bijiro da su ba; kamar Fikihul-Mukarin, wanda ya hado ra'ayoyin malaman mazhabobin sunna guda hudu da wasun wannan. Haka ya kasance yana da ra'ayi na masamman dangane da Ijma'I na furu'a, wanda ya saba da ra'ayin da ya yadu tsakanin malamai a lokacin. Wannan kuwa duk don amsa wasu bukatu ne da suka taso daga baya. Haka shi ya zo da cewa ka'idar nan ta Shura da ke Musulunci ita ce ka'idar Dukuradiyya wadda Turawa suka bijiro da ita bayan saukar Musulunci da karnoni.

Har ilau Sheikh Muhammd Abduhu, kamar Sayyid Jamaluddin, ya yi kokarin tabbatar da cewa Musulunci na iya zama akida mai shiryarwa, kuma tsaikon tunani na al'umma, ta yadda zai tabbatar musu da dacewarsu ta duniya da lahira. Haka nan ya yi ta kokarin bayyana wasu amfanoni na zamantakewa ga wasu ibadun Musulunci kamar salla, azumi, zakka, hajji da ciyarwa.

Shima, irin Sayyid Jamaluddin, ya yi aiki wajen samar da hadin kan duniyar Musulmi da ya nisanta daga bambance-bambancen launin fata, harshe, mazhaba da wurin zama.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next