Mutahhari Da Gwagwarmaya



Matsalolin al'umma da suka yunkurar da Sayyid Jamaluddin, kamar yadda Ustaz al-Shahid ya hakaito, sun ne:

1-Mulkin kama-karya dake gudana a cikin garuruwan Musulmi.

2-Jahilci da rashin wayewa dake addabar Musulmi, da matsanancin ci-baya a ilmance da yanayin zamantakewa da suke fama da su.

3-Yaduwar miyagun akidu cikin tunane-tunanen Musulmi, da nisantarsu da Musuluncin asali na hakika.

4-Rarraba tsakanin Musulmi ta fuskar mazhabobi da wasu al'amura da ba su shafi addini ba.

5-Mulkin-mallaka da ya yi musu kabe-kabe a gaba.

Sayyid Jamaluddin ya yi bakin kokarinsa wajen fitar da hanyoyin magance wadancan matsaloli. Ya yi amfani da abubuwan da suka samu a lokacinsa, irin su tafiye-tafiye, alakoki, laccoci, yada littafai da buga mujallu da kirkirar kungiyoyi da mu'assasosi dabam daban don aiwatar da ayyuka a wannan fanni. A takaice hanyoyin da Ustaz al-Shahid ya bayyana cewa Sayyid Jamaluddin ya bi wajen magance matsalolin duniyar Musulmi a lokacin sun ne:

1-Yaki da son-kan 'yan kama-karya.

2-Ganimantuwa da ilumma da sannai na zamani.

3-Komawa ga Musulunci na asali.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next