Mutahhari Da Gwagwarmaya



Shugabannin Gwagwarmayar Musulunci

Ba abu ne na jayayya ba, in ji Allama Mutahhari, cewa kowace irin gwagwarmaya na bukatar ja-goranci. Sai dai abin tambaya a nan shi ne: idan hakikanin gwagwarmaya ta zama ta Musulunci, manufofinta suka zama Musulunci; to yaya ya wajaba shugabancinta ya kasance? Wadanne irin mutane ne suke iya zama shugabannin ta?

Sai Shahid ya amsa da cewa: wannan bayyanannen abu ne. Shi ne cewa, bayan sun zama suna da siffofin shugabanci da ya hau kan kowane shugaba, su kuma dole su kara da:

1-Samun cikakkiyar masaniya da Musulunci.

2-Su san manufofi da falsafar dabi'u, da zamantakewa da siyasa.

3-Su zama suna da cikakkiyar masaniya da yadda Musulunci ke kallon rayuwa. Ma'ana nazarin Musulunci game da samuwa, halitta, Mahalicci, mafari da makoma. Da nazarin Musulunci a kan mutum da al'ummar dan Adam.

4-Su sami cikakken riska a kan tunanin Musulunci. Ma'ana riskar ra'ayoyin Musulunci kan yadda ya wajaba mutum ya zama, yadda ya wajaba ya rayu, yadda ya kamata ya gina kansa da al'ummarsa, wa zai yaka kuma da wa zai yi hamayya. A takaice dai su san amsar Musulunci kan hanyar mutum da yadda ya kamata ya bi ta.

Bayan Shahid ya kawo wadannan tanaje-tanaje na shugabannin gwagwarmaya, sai ya rufe da cewa:

Sanannen abu ne cewa ba wanda zai iya daukar nauyin irin wannan shugabanci da wadannan siffofin da sharudda sai ya zama ya tarbiyyantu ne daga kokon tunanin Musulunci; sai ya san AlKur'ani da Sunna, ya san furu'a da sannan Musulunci, cikakken sani. A kan wannan babu wanda ke iya shugabancin gwagwarmayar Musulunci sai malaman addini.[16]

MATSALOLIN GWAGWARMAYAR MUSULUNCI

Wani abu mai mahimmanci ga kowane yunkuri shi ne sanin yadda za'a magance matsalolin da ka fuskanto shi. Harkar gwagwarmaya ma na fuskantar irin wadannan matsaloli; wadanda, a ra'ayin Allama, aikin shugabannin ta ne su samar da kariya da rigakafin wadannan matsaloli. Allama ya kara da cewa:

Tabbas ne cewa matukar shugabanin gwagwarmayar Musulunci suka kasa magance matsalolin gwagwarmaya, ko suka yiwa al'amarin rikon-sakainar-kashi, to kuwa ko dai gwagwarmayar ta watse, ko ta sauya ta zama wata harka ta daban da ke haifar da akasin natijar da ake so.[17]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next