Mutahhari Da Gwagwarmaya



4-Imani da Musulunci da dogara da shi.

5-Yaki da mulkin-mallaka daga waje.

6-Kira zuwa ga hadin kan Musulmi.

7-Samar da ruhin jihadi a cikin al'ummar Musulmi.

8-Magance matsalar jin rauni a gaban Turawa da ya addabi Larabawa.

Har ila yau Shahid Mutahhari ya bayyana manyan manufofin Sayyid Jamauddin al-Afgani kamar haka:

1-Musulmi su zama wayayyun mutane, wadanda suka san zamunansu, suka kuma lakanci sana'o'in zamani.

2-Samar da wata al'ummar Musulmi 'yantacciya, wadda ta kubuta daga duk wani kang na harshe, yanki, mazhaba ko wani abu daban; wadda mutanenta suke 'yan'uwan juna.

3-Kubutar da Musulmi daga tabaibayin 'yan mulkin mallakan wajen da 'yan kama-karyan cikin gida.

4-Musuluncin asali na Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa'lihi), wanda ya tsira daga duk wasu jone-jone da shige-shigen ra'ayoyin mutane, ya zama shi ke hukunci cikin mutane.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next