Mutahhari Da Gwagwarmaya



A karshe Allama Mutahhari ya yi bayanin wasu yunkure-yunkure a tarihi da suka saba da wadanda ya ambata. Wadancan su na "ci-baya" ne, alhali wadannan na "ci-gaba" ne. ya bayar da misalin wadancan da yunkurin Asha'irawa a karnin hijra na hudu, da yunkurin Ikhbariyyun, daga 'yan Shi'a, a karnin hijra na goma, da yunkurin Wahabiyya a karnin hijra na goma sha biyu. Irin wadannan duk sun yi amfani ne da wani gurbi na tunani a tsakanin gama-garin mutane wajen cusa gurbatattun tunane-tunanensu game Musulunci cikin raunanan kwakwale.

GWAGWARMAYA TA FARKO A WANNAN ZAMANI

A tsakiyar karnin hijra na goma sha uku, daidai da karnin miladiyya na goma sha tara ne guguwar gwagwarmayar Musulunci ta taso a duniyar Musulmi; wadda ta game Iran, Masar Syria, Lebanon, Arewacin Afrika, Turkiyya, Afganistan da Indiya. Bayyanar wannan guguwa ya faru ne bayan lafawarta na tsawon karnoni. Bayyanar ta kuma na matsayin wani mayar da martani ne ga sabon salon yakin yamma ga raunanan kasashe, a ciki har da na Musulmi; wannan sabon salo kuwa shi ne 'Mulkin Mallaka'; wanda ya bullo ta hanyar siyasa, tattalin arziki da al'adu. Ita kuwa wannan guguwa sai ta zama wani nau'I na yunkurin 'wayarwa' da 'jaddada rayuwa' a duniyar Musulmi.

Sayyid Jamaluddin al-Afagani

Shahid al-Allama na cikin wadanda suke ganin cewa ko shakka ba bu Jamaluddin Asad Abadi, wanda aka fi sani Afagani, shi ne farkon wanda ya fara ta da wannan guguwa ta wayarwa a kasashen Musulmi. Shi ne wanda ya tona hakikanin matsalolin zamantakewar da ke addabar Musulmi, ya kuma bijiro da hanyoyin kubuta daga gare su.

Sayyid Jamaluddin ya ja-goranci gwagwarmayar kawo gyara ta fuskokin zamantakewa da tunani. Ya yi nufin samar da wani yunkuri a tunanin Musulmi wanda zai gyara rayuwarsu. Kuma wani abin sha'awa da Sayyid Jamaluddin, shi ne bai takaita da wani gari banda wani ba, ko wata kasa ko wata nahiya ban da wata ba. Ya kasance yana yawan tafiye-tafiye zuwa yankunan Asiya, Turai da Afrika; yana haduwa da kungiyoyi dabam daban a kowane gari. Har ma an ce a wasu garuruwan Musulmi ya shiga har cikin sojoji don ya yi musu tasiri.

Tafiye-tafiyen da Sayyid Jamaluddin ya yi zuwa kasashen Musulmi ne ya sa ya fahimci halin da duniyar Musulmi ke ciki. Yawonsa kuma a yankin Turai ne ya sa ya fahimci duniyar da ya ke ciki da kyau. Kamar yadda hakan ya sa ya gane hakikanin Turawa da manufofin shugabanninsu na goyon bayan kama-karya a kasashe,da mulkin-mallaka daga waje. Irin kafuwar da ya samu ne ya sa ya sami kyakkyawar masaniya da matsalolin duniyar Musulmi da kuma maganinsu.

Sayyid Jamaluddin ya yi matukar yin amfani da wadancan matsaloli biyu -wato kama-karya a cikin gida da mulkin mallaka daga waje- wajen wayar da kan mutane. Ya yi matukar yakar su da tsanani, wanda a karshe har sai da ya bayar da rayuwarsa a wannan tafarki. Ya yi imani da cewa yakar wadannan miyagun abubuwa biyu yana kasancewa ne kawai ta hanyar wayewar Siyasa da shigan Musulmi cikin harkokin siyasa ba ji ba gani.

Ta fuska ta biyu kuma Sayyid Jamaluddin ya yi imani da cewa idan har Musulmi suna son cimma manufofinsu da daukakarsu da darajarsu, to babu makawa sai sun koma zuwa ga Musuluncin asali. Ganin bayan bidi'o'I da karkacewa sharadi ne na asasi a kan wannan. Ya kasance yana kira zuwa ga hadin kan Musulmi; yana tona asirin wasu boyayyun makirce-makirce na 'yan mulkin mallaka wajen kawo munafunci da rarraba ta fuskar addini da ma wasu fuskokin da 'yan mulkin mallaka ke yi. Saboda tsananin rikonsa da ka'idojin hadin kai ya kasance ba ya fadar mazhabarsa da garin da ya fito duk yadda aka yi da shi. In an tambaye shi daga ina yake yakan ce daga garin Musulmi; mecece mazhabarsa yakan ce Musulunci.

Ya kasance yana ganin koda an sami wata alaka ta kusanci tsakanin masu kishin addini da mahukunta, matukar dai sun kiyaye kishin addini da kyakkyawar alakarsu da al'umma, to wannan na iya zama aiwatar da ka'idar nan ta furu'a ne mai cewa: ya halatta a yi amfani na'urorin makiyi don maslahar al'umma.[8]

A wani gefe, ra'ayin Shahid Mutahhari na iya kara bayyana game da gwagwarmayar Musulunci idan muka kalli yadda ya yabi matakan Jamaluddin Afagani; a kan haka yake cewa:

Wata baiwa da Sayyid Jamuluddin ke da ita shi ne bayan kasancewarsa wayayye, ya kuma kasance yana kiran mutane zuwa ga samun ilmomin zamani da amfana da wayewar Turwan yamma. Ya kasance yana yakar jahilci da ci-baya na kimiyya da fasaha da masana'antu. A daidai lokacin kuma ya riski hadarin dake tattare da tasirantuwa da wayewar Turawa. Don haka ya kasance yana kiran Musulmi da koyon ilumman sana'o'in Turawa tare da hamayya da tasirantuwa da tunane-tunanensu a kan duniya da al'amurra.[9]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next