Mutahhari Da Gwagwarmaya



Maganar da ake yi a nan game da tsayar da hukunce-hukuncen Allah ne. Magana ce a kan wani al'amari da masu aikin kawo gyara, 'yan gwagwarmaya da masu kishin addini suka dade suna furta shi. Shi ne zance a kan wajibcin tsayar da dokokin Allah a duk lokacin da al'umma ta kai matsayin da ba ta riko da dokokin Allah. Zance ne dake alaka da wanene zai iya aiwatar da wannan aiki na Annabawa da Manzanni. Shin kowane mutum na iya yin sa tare da irin yanayin da muke ciki na ruhi da halayya?

Daga nan sai ya shiga daukar wadannan sharudda daya bayan daya yana bayaninsu kamar haka:

1-Nisantar Sake da Sassuci: A nan Ustaz al-Shahid ya bayar da misali da shi mai maganar kansa. Inda ya ce akwai lokutan da aka nami Imam Ali (alaihis-salam) shi da ya kyale Mu'awuya a matsayin shi na gwamna don wata maslaha ta siyasa. Amma sam, Imam ya ki mika wuya da wannan bukata. Ya kira hakan da "sake da sassuci". A wasu lokuta kuma wasu mabiya da abokai sukan zo su yi ta ambaton Imam da lakabobi na yabo da sunaye iri-iri, tare da kau da kai daga kura-kuran da suka gani daga wasu ma'aikatansa; amma Imam Ali ya rika hana su ta mafi tsananin hanya, yakan ce musu:

Kar ku yi mau'amala da ni da neman sake (jan-hankali), kuma kar ku magana da ni da kalmomin da kuke amfani da su a kan masu girman kai.[20]

2-Nisantar Jirwaya da Tasirantuwa: Shahid al-Allama ya yi sharhin wannan da tasirantuwar dan gwagwarmaya da yanayin da yake son gyarawa. Ya bayyana cewa duk wanda ke son gyara raunin mutane, to ya wajaba ya tsarkake kansa daga wadannan illoli da rauni; kamar yadda mawaki ya fada:

Mara tsoron Allah dake horon mutnane da takawa

Kamar likitan dake ba mutane magani ne alhali ba shi da lafiya

Idan har a wasu lokuta mara lafiya na iya warkar da wani mara lafiyan, to a al'amarin ruhi ba haka abin yake ba, in ji Ustaz al-Shahid.

3-Yakar Gurin Bautar Mutane: Allama ya fassara wannan da 'yantuwar ruhi daga duk wani gurin biyayya da bautar mutane. Dan gwagwarmaya kar ya sa ran ganin mutane na bauta masa dabbaka dokokin Allah a doron kasa ba ya kasancewa a hannun masu irin wannan nau'I na guri.

Allah Ya ba mu sa'a baki daya. Walhamdu Lillahi Rabbil Alamin


[1] Shahid Murtadha Mutahhari, al-Harkatul-Islamiyya Fi Karnil-Rabi'u Ashar al-Hijri, shafi na 10.

[2] Ana iya samun haka a surar Bakara, aya ta 11 da ta 220; da Surar A'araf, aya ta 56,58 da 170; da Surar Hud, aya ta 88 da 111; da Surar Kasasi, aya ta 19.

[3] Shahid Murtadha Mutahhari, al-Harkatul-Islamiyya Fi Karnil-Rabi'u Ashar al-Hijri, shafi na 11.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next