Mutahhari Da Gwagwarmaya



Daga nan sai Shahid ya shiga kasafto matsalolin gwagwarmaya kamar haka:

1-Shigowar bakin tunane-tunane: wannan, in ji Allama, na iya shigowa cikin sahun 'yan gwagwarmaya daga makiya ko masoya. Daga makiya yana shigowa ne a lokacin da suka ga alamun nasara ga wannan harka, ko haduwar hankulan mutane zuwa gare ta, ko fifikonta a kan sauran kungiyoyi; to a lokacin da suka fahimci rashin yiwuwar rusa ta ta waje, sai su yi kokarin rusa ta ta ciki. Misalai a kan haka cikin tarihinmu na Musulunci na da yawa, Allama ya kawo wani sashi daga cikin. Ta hanyar masoya da mabiya kuwa, yana faruwa ne a yayin da wasu mabiya suka jahilci manufofin harka; ko suka rungumi wasu akidun Turawa suka yi kokarin basu siga ta Muslunci. Allama ya ambaci maganin wannan annoba da cewa shi ne ilmantar da mutane hakikanin Musulunci. Da daukar matakan da suka dace wajen ihtiyadi da kiyayewa sosai.

2-Zarbabiya: Dangane da wannan Allam Shahid ya bayyana cewa daukar madaidaiciyar hanya da matsakaicin matsayi a kowane abu yana da matukar wuya; domin, kamar yadda ya ce, matsakaiciyar hanya a tafiya na da matukar kunci. Don haka idan ba a kiyaye ba, za sami masu wuce iyaka da yawa a cikin harka, abin da zai iya haifar mata da matsaloli masu yawan gaske. Shagaltar da mutane da ilimi na matukar taimakawa wajen rage wannan hali na wuce iyaka. Imamai sun yi hani da gullanci da tsananin gaske; domin cutarwarsa ga addini bai kasa cutarwa nasibanci ba.

3-Rashin cika aiki: Wannan na bayyana ne so tari, in ji Allama, a lokacin da shugabannin gwagarmaya suka ja mutane har zuwa kawar da azzalumai; to a wasu lokuta bayan sun kau da fasadi, sai kawai su koma shagulgulansu, sun dauka cewa komai ya kare daga nan. A karshe sai wasu su zo su rike akalar al'amurra, a lokuta da dama ba su kan bi manufofin 'yan gwagwarmaya ba. Ustaz al-Shahid ya misalta musu yin haka da mutumin da aka kwacewa gona, sai ya yi ta wahala wajen kwato gonarsa, bayan ya kashe kudi da lokaci ya kwato ta, sai kuma ya ki noma ta ya bar wasu na nomawa. Ya ce abin da ya faru da shugabannin thauratul-Ishrin ke nan a Iraki, da shugabannin thauratul-Dostur a Iran, wadanda bayan sun yi nasara sai suka janye, a karshe wannan ya yi matukar taimakawa wajen jefa Iraki a halin da take ciki yanzu.

4-Rashin Bayyanannen Tsari na gaba: A kan wannan Allama Mutahhari ya bayar da wani misali mai kyau dake bayyana abin da yake nufi karara. Ya ce misali mu ne mu ke da wani gini da muke son mu rushe, saboda ya lalace muke so mu sake wani mai kayu a madadinsa. A nan zamu zama muna da surori biyu a kwakwalenmu; mummunar sura ta tsohon ginin nan, da kyakkyawar sura ta sabon da muke son yi. Dangane da mummunar sura, ba ya bukatar wani dogon bayani; domin mun san irin cutarwar da muke fuskanta. Amma game da sabon ginin da muke son yi, a nan dole ko dai mu sami injiniyan gini da zai yi mana wani tsari bayyananne; ko ya zama da ma muna da tunanin wani ginin da muka ga ingancinsa kuma mu ke son mu yi irinsa. To a bangaren gwagwarmaya, a kan sami wasu lokuta da wasu ke gabatar da kyakkyawan tsarin rushe zalunci da tsinge tushen barna; alhali ba su da wani bayyanannen tsari na gina adalci da islahi. Malaman addini su ne injiniyoyi, in ji Ustaz al-Shahid, wadanda al'umma ke jira su bayar da tsarin gini. Matukar kuwa suka kasa yin bayani da kowa ke iya gani game da abin da suke son ginawa, sai dai kawai fadar cewa: 'za mu gina muku mafi kyawun gini' to kuwa hakika za su bar wa al'umma wani gibi na shakka a kansu. Don haka dole ne kowace harka ta gabatar da tasre-tsarenta ga mutane su gani ba tare da wani boye-boye ba.

5-Rashin Kyakyawar Niyya: wani abu kuma da Allama ya sanya shi cikin annobobin gwagwarmayar tabbatar da addini shi ne wanda ke da alaka da ruhi. Wato niyya da kuduri. Allama ya ce:

Duk wani yunkuri na Allah, ya wajaba ya fara don Allah, ya kuma ci gaba don Allah. Kar ma'abuta gwagwarmaya su bari wani abu ya yi tasiri a cikin tunaninsu in ba Allah ba. Wannan ne kawai zai sa su dogara al'amuransu ga Allah.[18]

SHARUDDAN NASARAR 'YAN GWAGAWRMAYA

Allam Murtadha Mutahhari ya fitar da sharuddan nasarar gwagarmaya daga maganganun Imam Ali (alaihis-salam) . Imam ya fadi cewa:

Babu mai tsayar da horon Allah sai wanda ba ya sake da saussautowa, kuma ba ya rikida kuma ba ya bin gurace-gurace.[19]

Wajen sharihin wannan magana ce Ustaz al-Shahid ke cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next