Bidi’a A Cikin Addini



1-Cikakkiyar masaniya dangane da mutum.

2-Rashin duk wani amfani ga kafa dokar dangane da wanda yake kafa dokar.

3-Rashin la’akari da wata kungiya ko wasu masu karfi a cikin al’umma. Wadannan siffofin guda uku babu wanda yake da su kamar yadda ya dace Sai Allah madaukaki.

Majalisar dokoki kuwa da take jamhuriyar musulunci rawar da take takawa bai wuce fito da hukunce-hukunce ba daga tushensu ko kuma mu ce shirya abin da ya kamata a aiwatar a cikin hukuma.

3-Duk wani ketare iyaka wanda ya shafi kafa doka wani abu ne wanda aka yi hani a kansa, koda kuwa da ma’anar canza wani abu ne. Saboda haka kari ko rage wani abu a cikin addinin Allah haramun ne kuma ana kirga shi daga cikin bidi’a.

4- Kalmar bidi’a tana tabbatuwa yayin da ya kasance sabon abu ya kunshi wadannan siffofi da zamu ambata a kasa.

A-Wani aiki wanda yake sabo sannan da sunan addini ya kuma zama wani abu cikin addinin.

B-Rashin samun tushen wannan abin daga cikin Kur’ani ko Sunna ko hankali.

C-Yaduwar wannan abin a cikin al’umma a masatyin wani abu na addini.

5-Kur’ani mai girma yana daukar bidi’a wani nau’i na kirkira abu da dangana shi zuwa ga Allah, ta yadda ya zamana mushrikai suna halittawa kuma suna haramtawa su kuma jingina shi zuwa ga Allah, sakamakon haka ne aka yi Allah-wadai da su. Haka nan ma Kur’ani yake zargin yahudu da nasara a kan canza wani abu da suke daga cikin littafin Allah.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next