Bidi’a A Cikin Addini



Daga wannannan bayani zamu iya fahimtar cewa akwai wasu ayyuka daga cikin ayyukammu wadanda mai yiwuwa su zama halas ko haram, amma ba a kiransu bidi’a, kamar misalin kwallon kafa ko wani nau’i na wasanni. Irin wadannan sababbin abuwa a cikin rayuwa, sakamkon kasantuwarsu ba shigar da wani abu ba ne a cikin addini ba a kiransu da bidi’a.

A yau ga wadanda suka samu tasiri daga turawa al’adar hada maza da mata a taruka wani abu wanda ya zama ruwan dare, amma tunda masu yin wannan aiki ba su danganta shi zuwa ga Allah ba, don haka ba a kiran wannan bidi’a, duk da cewa a mahangar musulunci ya haramta.

Saboda haka zamu iya daukar sakamako a kan cewa ‘bidi’a tana kunshe da sanya wani abu a cikin addini. Saboda haka idan wani abu sabo ba a shigar da shi cikin addini ba wato ba da sunnan addini ake yinsa ba, ta yadda ba a jibinta shi zuwa ga Allah ko Manzonsa ba, wannan ba a kiransa bidi’a. Wannan kuwa babu bambanci ya kasance a mahangar shari’a ya halatta ne (kamar kwallon kafa) ko kuwa bai halatta ba kamar cakudar maza da mata.

2-Ya Kasance Ba Shi Da Asali Daga Kur’ani Da Sunna

Sharadin na biyu a cikin abubuwan da suke mai da abu ya zama bidi’a shi ne ya zamana wannan abin da aka sanya a cikin addini ba shi da tushe daga Kur’ani da sunnar Ma’aiki, ta yadda zai zama shi ne madogara wajen yin wannan sabon abin. Domin kuwa idan ya zamana yana da madogara daga Kur’ani ko Sunna to ba a kiransa bidi’a a cikin addini sai dai a ce zuwa da wani abu wanda yake a cikin shari’a wanda aka manta da shi yanzu kuma aka gano shi ya bayyana.

Wannan sharadi kuwa yazo a bayyane a cikin ma’anar bidi’a sannan kuma an kara karfafa shi a ilimince. Ta yadda suke cewa: “Bidi’a ita ce zuwa da wani abu a cikin addini wanda ba shi da madogara a cikin addinin, amma idan ba haka ba bai zama bidi’a ba”.

Saboda haka bisa ga dogaro ga wannan sharadi na sama da aka ambata zamu iya gane cewa da yawa daga cikin sababbin abubuwa wadanda suke a cikin rayuwa mutane a yau ba’bidi’a ba ce, duk da cewa ana dangana su zuwa ga addini. Domin kuwa wadannan sababbi abubuwa suna da tushe daga addini, saboda haka suna samun inganci ta fuskar samo asalinsu ne daga addini’duk da cewa ba a fili suka zo ba amma an fitar da su ne daga Kur’ani da Sunna.

A matsayin misali a yau sojojin duniya da na jamhuriyar musulinci ta Iran suna da manyan makamai domin kare kansu. Wannan al’amari na tanadar makamai bayan yana kara dora sojojin a kan makiyansu, kuma wani umarni ne na Allah madaukaki inda yake cewa a cikin Kur’ani mai girma: “Ku yi musu tanaji daga kayan yaki iya iyawarku, sannan ku tanaji dawakai masu kaifi ta yadda zaku tsoratar da makiyanku”[11].

A cikin wannan umarni guda biyu ne ya zo ta yadda daya daga cikinsu yake nuni da abu kebantacce da na gaba daya kamar haka:

1-Umarni na gaba daya: Shi ne iya yadda kuke iyawa ku tanaji karfi (duk wani nau’i na kayan yaki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next