Bidi’a A Cikin Addini



A cikin tarihi ana rubutawa cewa farkon bid’ar da sahabbai suka zo da ita bayan wafatin Manzo shi ne tankade garin alkama, wannan al’amari ne wanda yake sabo kuma da ba a yinsa, amma wannan ba ya daga cikin bid’ar da malamn fikihu suke cewa tana daga cikin manyan zunubbai. Saboda haka dole a bayyanar da cikakkiyar ma’anar bida’r da ake magana a cikin shari’a.

Amma bid’ar da malaman fikihu da akida suke magana a kanta kuma take daya daga cikin manyan zunubbai ita ce shigo da wani abu a cikin addini ta hanyar rage wani abu ko kuwa kara wani a cikin addini wanda bai zo ba daga Allah. Misali kamar yadda a kara wani abu a cikin kalmomin kiran salla ko kuma rage wani abu daga ciki. Ko kuma kara lokaci ko rage shi a cikin lokacin azumi sabanin yadda adini ya zo da shi wato daga bulluwar alfijr zuwa faduwar rana.

Amma masana suna bayyanar da ma’anar bidi’a kamar haka:

A-Bidi’a ita ce kari ko rage wani abu a cikin addini, sannan a dauki wannan abin daya daga cikin addini.[8]

B-Bidi’a ita ce kawo wani abu sabo a cikin addini alhali babu dalilin shari’a a kan halarcinsa. Amma idan wannan kawo sabon abin yana da asali a cikin shari’a to ba ‘bidi’a’ ba ce.[9]

C-Bidi’a ita ce farar da wani abu sabo a cikin addini. Tare sharadin cewa babu wani dalili ko asali daga addini da yake nuna halascin abin, ana kiran wannan bidi’a a cikin addini a tsakanin musulmi[10].

Muna iya wadatuwa da wadannan ma’anoni guda uku. Sannan mu manta da sauran ma’anonin da ba su da ma wani muhimmin bambanci da wadannan. Saboda haka daga wadannan ma’anoni zamu iya fahimtar cewa bidi’a tana da wasu rukunnai guda uku wadanda suke raba ta da ‘Sunna’.

 

1-Sanya wani abu a cikin addini

Duk wani kari ko ragi a cikin addini wanda zai sanya addini ya samu wani canji sakamakon hakan, sannan kuma a danganta wannan zuwa ga Allah ko manzonsa. Amma sabunta wani abu wanda zai sanya mutum ya samu wani canji a ruhinsa, ba a kiransa bidi’a. Amma mai yiwuwa ya kasance bai halatta ba amma ba a kiran sa bidi’a da wannan ma’anar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next