Bidi’a A Cikin Addini



2-Sannan kada ya zamana akwai wani amfanin da zai dawo zuwa ga mai kafa dokar.

3-Ya zamana ya tsarkaka daga duk wani neman matsayi ko daga wani bangarenci na wata kungiya.

Wadannan sharudda kuwa sakamakon bahsin da zamu yi nan gaba zamu ga cewa babu wanda yake da su sai Allah shi kadai mawadaci. Domin kuwa:

A-Mai kafa doka dole ya zamana yana da cikakkiyar masaniya dangane da mutum ta yadda zai san duk abin da yake damunsa da abin da yake bukata. Ta yadda sakamakon haka sai ya kafa dokokin da zasu daidaita shi su kuma shiryar da shi.

Sannan mai kafa doka dole ne ya san rayuwar zamantakewa tare da al’umma, ta yadda zai san ayyukan da ya kamata kowane mutum guda zai aiwatar a cikin al’umma, sannan ya san wanene a cikin ayyukansu zai amfanar da shi da kuma abin da zai cutar da shi a matsayin rayuwarsa ta zaman tare. Wannan kuwa babu wanda ya san hakan sai wanda ya halicci mutum ya san bukatunsa da matsalolinsa, shi ne wanda ya halicci mutum ya kuma san abin da yake bukata. A kan haka ne Kur’ani yake cewa: “Shin Allah bai san abin da ya halitta ba da kayau, alhali kuwa shi ne wanda ya san sirrin abin da ya halitta”.[1] Allah shi ne mahaliccin kwayoyin halitta da gabobin da suka hadu suka yi mutum, tabbas wanda yake haka shi ne ya fii kowa sanin abin da zai amfanar da cutar da mutum.

Shi ne sakamakon cikakken iliminsa ya san duk wani abin da zai gyara alakar da ke a tsakanin mutane, sannan ya san abin da kowa ya kamata ya aikata domin tabbatuwar laka mai kyau a tsakanin al’ummasannan ya san duk wani hakki na kowane mutum a cikin la’umma.

B-Sanin hakinin al’amura da kiyaye abin da zai amfanar da mutane yakan wajabta wa mai kafa doka ya tsarkaka daga duk wani neman amfanin kansa ko son kai wajen kafa doka. Domin kuwa siffar son kai nemar wa kai amfani takan sanya wani hijabi mai karfi tsakanin mai kafa doka da hakikanin al’amari, domin kuwa mai kafa doka duk yadda ya kasance mai son adalci mai son gaskiya to zai kasance cikin tarkon son zuciya idan har ya kasance yana da wannan siffar.

C-Kwadayi da kula da wasu manyan mutane da suke a wata kungiya mai karfi a cikin al’umma yakan sanya mai kafa doka ya kauce wa ka’ida wajen kafa doka ta yadda zai kafa doka ba tare da nuna bambanci ba. Sannan wannan zai hana shi ya zamana ya kafa doka kawai domin amfanin dukkan al’umma, wato duk abin da yake shi ne mafi alheri ga al’umma shi zai kafa doka a kansa.

Sannan tsoro da damuwa daga dokokin wasu masu karfi wannan kuwa daidaikun mutane ne ko kuwa wata kungiya ce, takan kasance kamar wata takobi a kan mai kafa doka ta yadda zata yi tasiri a kansa wajen kafa doka. Musamman sakamakon matsalolin rayuwar zamantakewa, wannan yakan sanya mai kafa doka ya zamana ya dace da guguwar masu karfi ta siyasa ce ko kuwa ta akida, wato ya zamana ya bayar da wuya ga wannan guguwar mai karfi da yake fuskanta. Idan kuwa ba haka ba dole ya yi shirin fuskantar matsaloli wadanda suka da dauri da makamantansa, ta yadda zai kauce wa wannan matsayi na kafa doka wasu su maye gurbinsa. Domin kuwa idan ma bai mika wuya ba to lallai ba shi da karfin da zai yi fito na fito da wannan barazanar da take fuskantarsa.

A nan ma Allah ne kawai wanda yake madaukaki mai kudra wanda ba ya jin tsoro ko shakkun wani ko kuma ya ji kwadayin wani abu, dimin dukkan sun koru daga gareshi (s.w.t), Saboda haka shi kadai ne yake iya kafa dokar da zata dace da abin da zai amfanar da mutane da kuma abin da zai iya cutar da su, sai ya kafa dokar da ta cancanta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next