Bidi’a A Cikin Addini



2-Umarni na biyu kuwa shi ne yana nuni ne ga tanadar dawaki masu karfi domin filin daga (a nan kuwa ya yi nuni ne ga wani nau’i na makami)

Saboda haka sayen duk wani nauyin makamin yaki na zamani, aiwatar da umarni ne na farko wanda yake nuna a yi wa sojoji tanajin manyan makamai na zamani. Saboda haka tare da la’akari da wannan aya muna iya danganta tanajin da muke wa sojoji da kayan yaki na zamani zuwa ga shari’a da addini, sannan kuma aikimmu ba zai zama bidi’a ba. Domin kuwa ba a ambaci wadannan makamai da nau’o’insu ba, amma bangaren umurnin aya ta farko yana nuni da tanajin wadannan makamai. Saboda haka samun irin wannan tushe daga addini yana tabbatar da ingancin hakan a addini.

3-Ya zamana ya yadu cikin al’umma: Daya daga cikin sharuddan kasancewar sabon abu ya zama bidi’a shi ne, ya zama ya yadu a cikin mutane. Duk da cewa wannan sharadi bai zo a wajen bayyana ma’anar ‘bidi’a’ ba amma hakikanin ‘bidi’a’ yana kunshe da shi. Sannan akwai abubuwa da yawa da suke nuni a kan hakan.

Misali ya zo a cikin ruwayoyin inda suke nuni a kan fito na fito da ‘bidi’a’ masu yin bidi’a babu shakka wadannan ruwayoyin sakamakon yaduwar wannan bidi’o’i ne a tsakanin al’umma ta hanyar masu yin wannan aiki.

Manzo mai tsira yana cewa: “Duk wanda ya zo da bidi’a a cikin wannan addinin zunubbin wadanda suka bi shi a kan hakan yana a kansa”[12]. Wannan ruwaya da makamanciyarta suna nuni ne a kan cewa tunanin kari ko ragi a cikin addini matukar bai wuce matsayin tunani ba wato bai kai ga aiki ba ta yadda kawai ya tsaya ne ga mai shi, wato bai yadu zuwa ga sauran mutane ba, to a nan haramun ne kawai amma ba bidi’a ba ce.

Tare da kula da wadannan sharudda da muka ambata na bidi’a muna iya fahimtar hakikanin ma’anar bidi’a sannan mu fahimci iyakokinta ta yadda zamu iya gane abin da ba ita ba.

 

Haramcin Bidi’a A Cikin Kur’ani Da Sunna

Bidi’a wani nau’i ne na shiga a cikin hakkin tafiyar da al’amura (rububiyya) domin kuwa al’amarin kafa doka ya kebanci Allah ne kawai, saboda haka duk wani nau’i na shiga a cikin tafiyar da al’amura yana da hukunci shiga cikin hakkin Allah madaukaki. Sannan jingina abin da ba shi da asali daga addinin zuwa ga Allah ko manzanninsa, yana daga cikin kirkira wa Allah da manzanninsa wani abu wanda ba daga garesu yake ba (Iftira).

Sakamakon haka ne Kur’ani yake Allah wadai da bidi’a. Misali dangane da mushrikai inda suka raba ranakun Allah ba tare da wani dalili ba, ta yadda suka sanya wasu ranaku halas wasu kuwa haram, sannan suka jingina wannan aiki nasu zuwa ga Allah, a kan haka ne Kur’ani yake cewa: “Shin Allah ne ya yi muku izini a hakan ko kuwa kuna kirkirawa ne ku dangana shi zuwa ga Allah?”[13].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next