Bidi’a A Cikin Addini



Malamai da masana da addinin musulunci kowane lokaci sun kasance suna kokari a kan hana shigowar bidi’a a cikin addini, sannan wannan ya wajaba a kansu domin kula da abin da wasu wadanda wasu daga cikin masu magana da yawon addini da marubuta, ta yadda zasu kula da abin da suke fada domin sukan yi amfani da kalmomi masu jan hankali domin su shigo da sabbin abubuwa a cikin addini. Sannan wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi kariya a kan addini duk inda yake, ta yadda addini zai kasance kamar yadda ya zo daga Allah madaukaki ba tare da wani canji ba. Kamar yadda ya zo daga Manzo kuma dukkan Sunna da Shi’a sun tafi a kan hakan cewa: Manzo ya ce wa al’umma da su koma zuwa ga Kur’ani da koyarwar Ahlul baiti (a.s) idan suka yi riko da wadannan abubuwa guda biyu, ba zasu taba bata ba daga hanyar daidai, inda yake cewa: “Na bar muku nauyi guda biyu littafin Allah da Ahlul baiti wadanda idan kuka yi riko da su ba zaku halaka ba har sai kun koma zuwa wurina a bakin tafki”.[20]

Sannan a wani hadisin an siffanta iyalan Manzo ne da jirgin annabi nuhu da cewa duk wanda ya shige shi ya tsira wanda kuwa bai shiga ba ya halaka domin zai nutse”.[21] Duk lokacin da al’ummar musulmi suka karbi addininsu daga iyalan Manzo tabbas zasu samu cikakkiyar shiriyar Ubangiji, sannan zasu tsira daga duk wata bidi’a da bin masu bidi’a.

Zuwa nan mun fahimci ma’anar bidi’a kuma mun gane bambancinta da sunnar Ma’aiki (s.a.w) sannan wannan bahsin zai zame mana matsayin mabudi domin yin amfani da shi a bahsoshimmu na gaba.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



[1]- Mulk:14.

[2] Dokokin zamantakewa:81(social law)

[3] Yusuf:40

[4] Tauba:31



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next