Bidi’a A Cikin Addini



A nan amsar wata tambaya guda daya kawai ya rage wannan kuwa ita ce, idan hakkin kafa doka kawai ya takaita ga Allah ne, to a jamhuriyar musulunci menene matsayin kafa dokar da ‘yan majalisa suke yi?

Amsar wannan tambaya kuwa ita ce, aikin ‘yan majalisa shi ne shirya ayyuka a karkashin dokokin na baki daya da musulunci ya zo da su, don haka ba suna kafa dokoki sababbi ba ne. Sannan babu wata kasa duk yadda ta kai wajen ci gaba wajen dokoki ta zamana ta wadatu da shirya abin da ya kamata ta yi (programs) Saboda haka a hakikanin gaskiya Majalisa wani wuri ne na shirye-shiryen abin da ya kamata gwammanati ta aiwatar karkashin dokokin addinim musulunci. Sannan ta nuna yadda ya kamata a aiwatar da wadannan dokokin acikinrayuwar dan Adam ta yau da kullum.

 

Bidi’a A Cikin Addini

Kamar yadda yake kafa doka hakki ne kawai na Allah madaukaki sannan babu wani wanda yake da wannan hakkin ta yadda zai kafa wa wani mutum kowata al’umma doka. Haka nan babu wani wanda yake da ikon ya kara ko ya rage wani abu a cikin dokokin da Allah a saukar ta hanyar wahayi. Saboda haka sanya hannu a cikin dokokin da Allah ya saukar ta hanyar ragi ne ko kari, wannan shi ne ake kira da “Bidi’a” a cikin addini. Saboda haka mutumin da ya yi haka ya yi bidi’a a cikin kadaita Allah a cikin kafa doka wanda muka yi maganarsa a sama.

Sakamakon barnar da ke akwai wajen (bidi’a) ko sanya hannu wajen kafa doka ya zamana daya daga manyan zunubbai wanda wannan bahsin da muke cikinsa yake dauke da cikakkiyar ma’anar “Bidi’a” wanda yake daya daga cikin muhimman abubuwan da zamu yi magana a kai nan gaba.

Ma’anar Bidi’a a harshen larabci shi ne, yin wani abu sabo wanda yake da ba a yinsa. Saboda haka duk wani sabon abu wanda yake da ba a yinsa ana kiransa “bidi’a”. [6]

Dabi’ar Mafi yawan mutane Suna son sabon abu, sannan ba su son rayuwar da take da yanayi iri guda babu canji. Sakamkon haka ne ya sanya masana ginin gidaje a kodayaushe suke kokari wajen samar da zane da nau’oi’in gidaje kala daban-daban, sannan kalar tufafin da mutane suke sanyawa kullum yana samun canji, dukkan wadannan ta fuskar lugga ana kiran su da Bidi’a. A kan haka ne ma Kur’ani mai girma yake ambatar Allah madaukaki da “Mai kirkiro sammai da kassai”[7]. Domin kuwa shi ne ya kirkiro sammai da kasai ba tare da ya ga makamantansu ba kafin nan, Wani abu ne sabo wanda a da bai gabata ba.

Amma a nan akwai wani abu wanda ba mu fada ba dangane da ‘bidi’a’ domin kuwa bidi’a da wannan ma’ana ba ita ce ba ce muka yi magana ba a kanta a bahsin mu na baya wacce take an haramta kamar yadda muka yi bayani.

Domin kuwa musulunci ba ya hani a kan sababbin abubuwa a cikin rayuwar daidaiku da zaman tare. A yau dan Adam dangane da yanayin rayuwrsa yana da abubuwa sababbi wadanda ba a taba yinsu a tarihi, kamar abin da ya shafi gine-gine da tufafi da dai makamantansu. Duk da cewa wadannan a mahangar ma’ana ta kalmar ‘Bidi’a’ suna iya shiga a ciki amma ba su daga cikin bidi’a wacce ake magana wacce take daya daga cikin manyan zunubbai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next