Halayen Imam Ali a.s



a- Kasantuwarsa shi mutum ne musulmi tsantsa cikakke tun daga farko, domin bai bi wanin Allah ba, kuma bai kauce daga aikata hukunce-hukuncen shariط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ar musulunci ba a cikin rayuwarsa, ya aikata su cikakkiyar aikatawa.

b ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ“ Saboda shaidar da Kurط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ani mai girma ya yi masa a game da Isma a cikin aya mai zuwa (Allah yana son ya tafiyar da dauda daga kanku Ahlul-Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa)[11] Imam Ali (a.s) shi ne na biyun Ahlul bait (a.s) wadanda aka ambata a cikin wannan aya mai girma.

c ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ“ Saboda shaidar da Annabi (s.a.w) ya yi masa a game da Isma a cikin hadisai, kamar: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali. Kuma har abada ba zasu rabu ba har sai sun zo sun same ni a tafki (a gefen alkausara".

Kuma ya kasance wanda ya fi dukkanin Masulmi sanin shariط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢a, hakan kuwa saboda shaidar da Annabi (s.a.w) ya yi masa a game da hakan a cikin irin wadannan hadisai nasa masu zuwa:

1. Ni ne birnin ilimi Ali kuma kofarsa

2. Wanda ya fi ku sanin hukunci shi ne Ali

Sai dai cewa wasu dalilai na tarihi sun hana shi karbar mulki, sai ya fuskanci tafiyar da harkar wayar da kan mutane da kuma daidaita tafiyar da shaط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢anonin daula a duk lokacin da maslaha ta gaba daya ta bukaci hakan. Hakan kuwa saboda kiyaye hadin kan Musulmi da rashin rarrabuwarsu. Kuma saboda tallafa wa alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ummar addinin Musulunci.

Bayan kashe Usman dan Affan a shekara ta (35 bayan hijira) Imam Ali (a.s) ya karbi halifanci. Kuma daga cikin muhimman ayyuka na gyara wadanda ya yi su akwai abubuwa masu zuwa:

1. Tsige gwamnonin da suka gabata (na lokacin Usman) da hukunta su, saboda ayyukan da suka aikata wadanda suka saba wa shariط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢a.

2. Yin watsi da tsarin raba dukiyar haraji wanda Umar dan Khaddab ya kirkire shi kuma Usman ya tabbatar da shi, Mayar da tsarin kamar yadda yake a lokacin Annabi (s.a.w), ta yadda rabon dukiya ya kasance a bisa asasin daidaitawa da rashin bambanta mutane a wajen rabon.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next