Halayen Imam Ali a.s



Wanan kissa tana nuna cewa; Talauci ya kawu gaba daya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta Imam Ali (a.s) da ya ga talaka guda daya mai bara kuma ba ma musulmi ba sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al'ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da ba ya riko da musulunci, domin kada a samu talaka a kasar musulmi ko da kuwa mutum daya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yaki da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yaki da talauci ta kuma daukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu matukar suna karkashin daular.

Haka nan musulunci ya dauki dan Adam da kima matuka ko da kuwa bai musulunta ba, sai dai duk wanda ya taba musulmi ya kashe su to shi kadai ne musulunci ya yarda musulmi su taba, don haka ne zamu ga a rayuwar Manzon Allah (s.a.w) bai taba kai hari kan mutanen da ba su suka fara kai masa hari ba. Kuma idan mutanen wani gari suka kai masa hari to bai taba yakar wasunsu na wani garin daban ba ko da kuwa addininsu daya ne, sai dai ya rama kan wadannan dai da suka kai masa hari kawai.

Duk da a rayuwar musulunci an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame. Don haka ne ma adadin wadanda ake kashe wa bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu. Wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba. (Littafin Tafarkin Rabauta: Fasalin; Aiko Annabi Mai Daraja (s.a.w).

Musulunci bai taba yarda da zaluntar wani mutum ko wani mai rai ba, kai hatta da barnar abinci da lalata wuri da lalata kasa ya hana balle azabtar da dan Adam ko kashe shi, ya kuma sanya kalma mai dadi da zaka gaya wa dan'uwanka mutum ya yi farin ciki a matsayin sadaka. Don haka ne ya soki mai lalata kayan gona da dabbobi, ya kira shi mai yada fasadi da barna, balle kuma mai isar da cutarwa ga mutum. Saboda haka ne ma muka samu dukkan matsalolin da muke ciki a yau musamman a kasashenmu sun taso daga rashin fahimtar musulunci ne, sai dan Adam ya kasance ba shi da wata kima.

Mun rasa ilimi ta yadda yawancin mutanenmu suna rayuwa a matsayin masu karancin ilimi ko ma ba su da shi saboda kawai yarenmu ba a yarda ya zama yaren ilimi ba, sai wannan karancin ilimin da rashin lamunin rayuwar suka haifar mana da rashin ganin kimar dan Adam. Muna iya ganin yadda aka kashe mutane babu imani, ko tausayi, ko hankali, kamar yadda Aljazira ta nuna a rikicin da ya faru a Maiduguri, ta yadda aka kashe mutanen da su ba ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¥â€œYan boko haramط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â‚¬إ’ ba ne, (kai ko da ma su ne ya kamata a kai su kotu domin doka ta zartar musu da hukuncin da ya dace ne). Har ma mai harbin ana gaya masa kada ya lalata bulet, kuma ya bar kai domin ana bukatar hular, wannan lamari mai ban takaici ya yi nuni da cewa; hatta da alburushi da hula sun fi dan Adam kima.

Sai ga maط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢aikacin da aka dauka aiki domin ya kare alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma yana harbe su ba su ji ba su gani ba, ana biyansa albashi da kudin alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma domin ya kare ta, amma sai ga shi hatta da raunanan mutane kamar guragu yana kamowa yana harbewa. Kuma idan dai ba a dauki mataki kan wadanda suka yi wannan ba, to tabbas wata rana shi wanda ya sanya su yin hakan zasu yi wa danginsa ko shi ma ta fada kansa. Domin idan rashin hankali, da rashin imani, da kekashewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin doka, suka yi jagoranci, to babu makawa zasu shafi kowane mutum ne. Idan rashin tsoron Allah da tunawa da cewa za a mutu a koma ga Allah ya yi hisabin dukkan abin da muka yi ya mutu murus, to sakamakon da za a samu kenan.

Musulunci ya sanya lamunin rayuwa ta hanyoyi masu yawan gaske, sai ya shimfida dokokin da zasu wadatar da dan Adam kamar zakka, humusi, sadaka, Baitul mali, kyauta, da ayyukan jin kai, sannan ya yi matukar gaba da jahilci da ba a taba samu ba a rayuwar dan Adam, sai ya tilasta neman Ilimi ko da kuwa a kasar Sin ne. Musulunci ya yi gaba da rashin ganin kimar dan Adam matuka, har ma ya ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¹آ©yanta bawa saboda ubangidansa ya yanke masa alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢aura. Kai hatta da iradar yara da ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¹آ©yan mata yayin zabin wanda zasu aura ya ba ta kariya. Sannan a fili yake hatta da addini bai tilasta kowa riko da shi sai wanda ya ga dama.

Sannan musulunci bai taba yarda da zubar da jinin mutum ya tafi a banza ba, don haka ne ma muke kira da gwamnati da ta biya diyya ga iyalan wadannan mutanen da aka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba, kai hatta da kisan kare dangi da aka yi wa musulmi da sunan baki a Jos a watan Safar 1431 muna neman a biya su diyyar wannan balaط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢in da ya fada musu. Jinin mumini ba ya faduwa haka banza ya wuce sai an biya diyyarsa, kuma ya hau kan gwamnati ne ta mika diyya ga danginsa, duba wannan misali mai zuwa da zai nuna maka matukar kima da sakon Muhammad (s.a.w) yake bai wa dan Adam kamar haka:

Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: Yayin da Sayyidi Ali (a.s) ya rusa rundunar Dalha da Zubair (r) sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu, sannan sai uwar ta mutu. Sai Imam Ali (a.s) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?. Sai suka ce: Tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu. Sai ya tambaya: Waye ya riga mutuwa a cikinsu?. Sai suka ce: Danta ya riga ta mutuwa.

Sai ya kira mijinta baban yaro mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar, sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi -barinsa- ya mutu. Ya ce: Wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara. (Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next