Halayen Imam Ali a.s



Kuma ya umarce shi da rike zuciyarsa a lokacin shaط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awance-shaط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awance, ya cire ta (ya kawar da ita) a lokacin sabo, domin ita zuciya mai yawan umarni ce da mummuna ban da wacce Allah ya yi wa rahama.

3. Daga cikin gajerun maganganun hikimarsa:

1. Ka gode wa wanda yake tsananta maka kuma yake yi maka waط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢azi, ba wanda yake tsarkake ka ba kuma yake yabon ka.

2. Ashararan mutane suna bin munanan ayyukan mutane su kyale kyawawan ayyukansu kamar yadda kuda yake bin gurare marasa tsafta.

3. Ka kiyayi mai aikata mummunan aiki, domin shi kamar takobi ne mai guba kallon sa yana faranta rai aikinsa kuma ya munana.

4. Ka guji bayar da uziri, domin takan yiwu wani uzirin ya tabbatar da hujja a kan maط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢abocinsa koda kuwa shi ba mai laifi ba ne.

5. Kada ka yi murna da faduwar waninka, domin kai kanka ba ka san abin da kake aikatawa ga wasu kwanaki naka ba.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next