Halayen Imam Ali a.s



1. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimin harshen larabci da adabobinsa.

2. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimomin akidar Musulunci.

3. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen Ilimomin shariط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ar Musulunci.

4. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen tarihin farkon Musulunci da Jahiliyya da al'ummomi na da.

5. Daukar sa a matsayin madogara da ake komawa gare shi wajen da yawa daga cikin Ilimomi kamar; Tarbiyya, da Halaye, da Shugabanci, da Halayyar Mutum, da Zamantakewa, da kuma Siyasa.

Nahjul balaga yana kunshe da: Hudubobi da kuma abubuwan da aka ciro daga maganganun Imam Ali (a.s) guda 236, Wasiku guda 79, Maganganun hikima guda 480. Daga cikin kyawawan abubuwan da suke ciki akwai: hudubar tauhidi, da wasiyyar Imam Ali ga dansa Hasan (a.s), da kuma umarnin Imam Ali ga Malikul Ashtar gwamnansa a Masar (Misra).

Daga Nahajul Balaga; Daga cikin wasiyyar Imam ga dansa Hasan:

Ya kai dana ina yi maka wasiyya a game da tsoron Allah, da lazimtar umarninsa, da kuma gyara zuciyarka da ambatonsa, da kuma riko da Igiyarsa, kuma wace alaka ce mafi aminci tsakaninka da Allah idan ka yi riko da ita?

2. Daga cikin umarnin Imam ga Ashtar:

Wannan shi ne abin da bawan Allah Aliyyu Amirul muط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢uminin ya umarci Malik bn al-harith al-ashtar, a cikin umarninsa wanda ya yi masa a lokacin da ya nada shi gwamna a Masar: domin tattara harajinta, da yakar makiyinta, da gyara mutanen cikinta, da kuma gyara garuruwanta.

Ya umarce shi: da tsoron Allah: da fifita da'arsa, da bin abin da ya yi umarni da shi a cikin littafinsa na daga abubuwan da ya wajabta, da kuma sunnoninsa, wadanda babu wanda zai rabauta sai ta hanyar bin su. Kuma babu wanda zai tabe sai ta hanyar kin su da tozartar da su. Kuma ya umarce shi da ya taimaki Allah (s.w.t) da hannunsa da zuciyarsa da harshensa, domin shi madaukaki ya dauki nauyin taimakon wanda ya taimake shi, da daukaka wanda ya daukaka shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next