Halayen Imam Ali a.s



Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen wasiyyin annabi Muhammad (s.a.w) kuma halifansa Imam Ali (a.s) da rayuwarsa. Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Imam Ali ya karbi jagorancin alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma bayan kashe Usman dan Affan a wani tawaye da alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢ummar musulmi suka yi masa suna kafirta shi, wannan lamarin bai yi wa munafukai dadi ba, don haka sai suka ga ya kamata su dora abin a wuyan Imam Ali (a.s) domin su samu jin dadin yakarsa da kashe shi da dukkan wani salihi, da kuma zuriyar manzon Allah (s.a.w) wanda shi ne babban makiyinsu.

Imam Ali (a.s) ya samu kansa a cikin wani yanayi maras dadi na rayuwar alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma da tattalin arzikinsu na rayuwa, da dukkan abubuwan da ya kamata su mora, domin ya tarar da dukkan dukiyoyin musulmi wanda ya rigaye shi ya bayar da ita ga wasu tsurarun mutane da yawancinsu Banu Umayya ne da ط£آ¢أ¢â€ڑآ¬ط¹آ©yan korensu wadanda suka shahara da gaba da manzon Allah (s.a.w).

Kuma wanda ya rigaye shi ya kebanci arzikin kasa ya bayar das hi ga wanda manzon Allah (s.a.w) ya tsine musu ya yi umarni da kashe su duk inda suke, sai gas hi sun kasance dukiyar alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma gaba daya ta koma hannunsu. Suna fasin da dukiyar Allah kamar dai yadda Imam Ali (a.s) ya siffanta a cikin hudubarsa ta Shakshakiyya a littafin Nahajul-balaga.

Sai ya daidaita dukiya da kyauta tsakanin mutane, ya daidaita su kamar yadda yake a lokacin manzon Allah (s.a.w) wanda wannan lamari ne da an dade da mantawa das hi tun lokacin manzon Allah (s.a.w). Imam Ali (a.s) yana cewa: Kuraishawa sun tsorata ni ina karami, sun dasa mini gaba ina babba.

Kuma rashin jin dadin canje-canjen da yake yi shi ne ya sanya aka kafa masa gaba mai tsanani kamar yadda yake a tarihi musamman wasu da ake gani a matsayin manya kamar Dalha da Zubair da Aط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢isha, sannan kuma ga munafukai a Sham su kuma da tasu gabar ta kin musulunci.

Imam Ali (a.s) ya yaki kuraishawa suna kafirai, kuma ya yake su suna munafukai, kamar yadda ma'aikin Allah (s.a.w) ya yi masa alkawarin hakan.

Game da tafiyar da dukiya kuwa ya yi wa musulmi jagoranci ne irin na lokacin manzon Allah (s.a.w), ya kasance yana cewa: "Da dukiyar nan tawa ce da na daidaita tsakaninsu, yaya kuwa, alhalin wannan dukiya ta Allah ce, kuma bayar da dukiya ba bisa hakkinsa ba barna ne, kuma yana daukaka mai yin haka a duniya, kuma ya kaskantar da shi a lahira, ya girmama shi gun mutane, ya kaskantar da shi gun Allah. Don haka ne ya yi kokarin samar da al'ummar da masu hannu da shuni ba su mamaye arzikin kasa ba, kuma ba a samu danniyar gurguzu ba.

A kasashenmu an samu wannan lamari ya yi kamari matuka da gaske, mai daraja shi ne wanda ya fi kowa satar kudin al'umma da danne hakkinsu yana raba wa sauran ashararan da suke jagorancin mutane tare, ana kashe mu raba da dukiyar al'umma, da wannan ne sai matsayinsa ya karu gun masu jin dadin kasa, girmansa ya karu gun masu danne hakkokin al'umma, amma wurin Allah kaskancin wulakantuwa a wuta yana jiran sa!.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next