Halayen Imam Ali a.s



Yana da falaloli da darajoji da ba zasu kirgu ba, ya kasance farkon wanda ya yi imani da Manzon Allah (s.a.w) kuma bai yi shirka da Allah ba koda sau daya, bai yi sujada ga gunki ba, don haka ne ma ake ce wa da shi; Allah ya girmama fuskarsa. Kuma yana tare da nasara a dukkan yakokinsa, bai taba gudu ba koda sau daya, shi mai kai hari ne ba mai gudu ba, bai taba ba wa yaki bayansa ba, bai taba gudu ba, kuma kyakkyawan hukuncinsa ya kai matuka har Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mafi iya hukuncinku shi ne Ali (a.s)[6].

Kuma saboda yawan iliminsa ne Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne birnin ilimi Ali kuwa shi ne kofarta"[7]. Kuma saboda lizimtarsa ga gaskiya ya ce: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali"[8].

Ya kasance mai adalci ne a jagorancinsa ga al'umma, mai rabawa mutane arziki da daidaito, mai nisantar kwadayin duniya. Ya kasance yakan zo Baitulmali sai ya duba abin da ya taru cikinta na zinare da azurfa yana cewa: "ya ke yalo! Ya ke fara! Ku yaudari wanina"[9]. Sannan sai ya rarraba wa mutane har sai babu abin da ya rage, yana tausaya wa miskinai, yana zama da talakawa, yana biyan bukatu, yana fadar gaskiya, yana hukunci da adalci, yana hukunci da abin da Allah ya saukar.

Yana aiwatar da hukunce-hukuncen Allah, yana kuma tafiyar da ayyukan Manzon Allah (s.a.w) har sai da alheri da albarka da yalwa suka mamaye kowa, da dukkan kasashe da dukkan garuruwa.

A takaice, ya kasance kamar Annabi (s.a.w) a dukkan siffofi da kyawawan halaye sai dai a wahayi da annabta, don haka ne Allah ya sanya shi kamar Annabi yake a komai banda annabta kamar yadda ya zo a ayar nan ta mubahala[10].

Imam Ali ya samu tarbiyya a gidan Annabi Muhammad (s.a.w) tarbiyyar da Annabi (s.a.w) a cikinta ya tanadar masa daukan nauyin daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awarsa ta Musulunci, da kuma daukar sakonsa mai tsarki.

Imam Ali (a.s) ya musulunta ne a lokacin da Annabi (s.a.w) ya kiraye shi zuwa Musulunci, a sa'ilin da Annabin ya dawo daga (kogon hira) yana dauke da sakon Musulunci zuwa ga mutane gaba daya.

Kuma addinin musulunci ya kasance addini na farko wanda Imam Ali (a.s) ya karba, domin kafin Musulunci bai karbi wani addini ba daga cikin addinan jahiliyya da kuma kafirci.

Kuma bayan musuluntar Imam Ali (a.s) sai Annabi (s.a.w) ya shiga shirya shi domin daukan nauyin daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awa, musamman ma nauyin daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awa na tunani da ilimi. Hakan kuwa a tsakanin lokaci mai tsayi na rayuwar daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awar a matakinta na sirri.

Hakika rayuwar Imam Ali (a.s) gaba dayanta Musulunci ce. Ta yadda ya bayar da dukkan abin da yake da shi har karfinsa a tafarkin daط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢awar Musulunci.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next