Halayen Imam Ali a.s



Imam Ali (a.s) ya sanya himma matukar wurin yakar fatara da talauci daga cikin alط£آ¢أ¢â€ڑآ¬أ¢â€‍آ¢umma, ya zo cewa ya aika da wani gwamna Afrika, bayan wani lokaci sai ya aiko masa da wasika yana cewa dukiya ta yi yawa gunmu, me zamu yi da ita? Sai Imam Ali (a.s) ya ce masa ka ba wa talakawa ita domin su wadata, sai ya sake aiko da wata wasika wani lokaci zuwa ga Imam (a.s) cewa talakawa sun wadatu kuma har yanzu akwai dukiya mai yawa me zamu yi da ita? Sai Imam Ali (a.s) ya aiko masa da cewa ka aurar da gwagwarensu da wannan dukiya, sai ya aurar da gwagwarensu, sannan sai ya aika da ragowar dukiya zuwa ga Imam (a.s).

Dukkan wannan yana iya sanya dukkan dan Afrika mai 'yanci yin tunani da zarar ya tsinkayi mazhabar Ahlul Baiti ya san abin da yake cikinsa sai mu ga ya karbe shi, kuma ya yi riko da shi ba tare da wani kokwanto ba, domin yana ganin arzutar duniya da lahira a cikinsa fiye da yadda yake gani a waninsa. Don haka ne ma a wannan gomomin karshe na rayuwar jama'ar Afrika zamu ga miliyoyin jama'ar Afrika sun rungumi mazhabar Shi'a domin sun sami kofar birnin ilimi a cikinsa a wannan mazhaba, da kuma rayuwa mai sauki, musamman ga wanda ya samu dacewar bin sa bisa hukunce-hukuncensa, domin kuwa mun karanta yadda halin yalwa da rayuwa mai dadi ya kasance a hukumar shugaban masu kadaita Allah Imam Ali (a.s).

Haka ne yayin da tunanin Ali da aikin Ali ya yi hukunci da koyarwar Ali to al'umma zata rayu rayuwa mai dadi, domin aikinsa aikin Allah ne da ilimin da Allah ya ba shi, kuma shi Imam Ali shi ne tafarki madaidaici, kuma hujjar Allah a kan mutane gaba daya.

Mu sani Ali (a.s) rahamar Allah ce kan talikai wacce wannan rahamar ta gangaro daga manzon Allah (s.a.w) wanda ubangiji madaukaki yake cewa game das hi: "Ba mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai" (Anbiya: 107), sai wannan rahamar ta biyo ta hannunsa. Rahamar Allah ita ce abu na farko da ya bayyana ga bayinsa bayan bayyanar sunansa Allahu, don haka ne ma rahamarsa ta yalwaci kowane abu. Rahamar Allah a nan ta mamaye dukkan janibin halitta a samuwarta, da kuma tsarin rayuwarta da aka fi sani da Shari'a.

Manzon Allah (s.a.w) rahama ne a Shari'a da ma'anarta mai fadi da ta shafi siyasa, tattalin arziki, zaman tare, tsaron al'umma, yalwar al'umma[1], rayuwar auratayya, hakkokin yara da na mata, da raunanan mutane, hukunce-hukuncen ibadoji da mu'amaloli, kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma, ilmantar da al'umma gaba daya ta yadda ba za a samu jahili ko da daya ba, samar da mazauni da matsuguni ga kowane mutum. Rahama ce ga dukkan talikai da tsarin da zai samar da adalci a cikin al'ummu duk duniya baki daya, da ta yalwaci kowane abu, balle kuma dan Adam mai kima da daraja. Don haka ne yayin da duniya ta kasance cikin duhu sai garinta ya waye da wanda Isa dan Maryam (a.s) ya yi wasiyya da zuwansa Muhammad (s.a.w).

Rahamar ba ta tafi ba don wafatinsa, domin rahama ce mai fadi da ta yalwaci kowane abu har alkiyama ta tashi, don haka ne ma ya zaba mata mahalli har goma sha biyu da zasu kasance bayyanar rahamar bayan wucewarsa. Ita siffa ce mafificiya ga Manzon Allah, Suna ne da Allah ya tsaga shi daga gareshi ya yafa masa shi, don haka ne ya zamanto rahama ga dukkan talikai da rahmaniyyarsa, rahama ga muminai da rahimiyyarsa da ta tsattsago daga rahamaniyyarsa.

Sai ya kasance yana da fifikon da babu wani mahaluki da ya taka shi, wannan matakin shi ne matakin "Hamd" wanda alaminsa shi ne "Tutar Hamd", sai ya sanya mai rikon wannan tutar shi ne wasiyyinsa Ali (a.s), yana cewa da shi: "Kai ne mai rikon tutata duniya da lahira". (Kanzul Ummal na Muttaki Hindi, Bahanife: J 13, Hadisi: 36476). Sai Manzon Allah ya taka matsayin "Hamd", Alinsa kuwa yana kan "Tutar Hamd", don ya yi nuni da cewa ga kofarsa nan da duk wani da ya wuce ba ta nan ba, to ba zai iso gunsa ba.

Kasancewarsa rahamar Allah ga bayi, kuma wanda ya taka mataki mafi girma na "Hamd=Godiya", don ya kasance mai yawan godiya ga Ubangijinsa, ibadarsa ba don tsoron wuta ko kwadayin aljanna ba, wannan ita ce ibadar bayi da masu kwadayi, amma ibadarsa ta kasance don godiya ce ga Allah. Sai ga tsokar jikinsa Zahara (a.s) take nanata cewa da Ubangiji ya azabtar da ita a wutarsa, da ta riki tauhidinta a hannu.

Imam Ali (a.s) kuwa wanda yake rike masa "Liwa'ul Hamd = Tutar Godiya" yana munajati da Allah yana cewa: Kuma wallahi! da ka sanya ni a cikin azaba tare da makiyanka, ka hada ni a wuta a tsakanin wadanda bala'inka ya fada wa, na rantse da girmanka ya madogarata jagorana, ina mai rantsuwa mai gaskatawa, matukar ka bar ni ina magana, to zan daga murya zuwa gareka tsakaninsu -'yan wuta- da muryar masu buri, kuma wallahi sai na kira ka ina kake ya masoyin muminai, ya matukar burin masana, ya mai taimakon masu neman taimako, ya masoyin zukatan masu gaskiya, ya Ubangijin talikai! (Muhasabutun Nafs: Kaf'ami; S: 187).

Sai manzon rahama (s.a.w) ya gadar da wannan rahamar ga wasiyyai, da wannan ne sayyidi Ali (a.s) yake cewa: "Ni bawa ne daga bayin Muhammad" (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449). Sai wadancan haskaka goma sha biyu da 'yarsa Zahara (a.s) suka kasance feshi daga rahamar Allah ta hannun Muhammad (s.a.w) bawansa, Rininsu da saninsu na Allah ne. (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next