Imamanci Da Nassi2



Ahlussunna sun ce wanda ya fadi haka shi ne Sa’ad dan Abi Wakkas ranar shura, Shi’a kuma sun tafi a kan Abu ubaida ne bayan Sakifa, kowanne ne gaskiya dai muhimmin abu ne wanda ya shahara da kowa Sunna da Shi’a suke rawaito wa kamar yadda Ibn Abil Hadid wanda yake Sunna kuma Bamu’utazili yake rawaitowa[43].

10- Fadinsa: “Ya Ubangiji! ni ina hada ka da kuraishawa da wanda ya taimaka musu, sun yanke zumuncina sun karanta matsayina, sun hadu a kan kwace mini abin da yake nawa ne, sannan suka ce: Ka karba da gaskiya ko ka bari da gaskiya[44],

11- Fadinsa: “Amma bayan haka… Yayin da Allah ya karbi ran annabinsa (S.A.W) sai muka ce mu ne ahlinsa masu gadonsa zuriyarsa majibinta al’amarinsa ba wani ba, ba mai yi mana jayayya kan shugancin Muhammad, kuma kada wani ya yi kwadayin hakkinmu, sai mutanenmu suka mike suka kwace mana hakkinmu na shugabanci, sai ga shugabancin a hannun waninmu…â€‌.

Wannan duk yana daga hudubobin da imam Ali ya yi a Madina a farkon shugabancinsa a lokacin bai fi watanni da karbar halifanci ba[45].

12- Fadinsa: “Amma kwace mana wannan matsayi wannan wani abu ne da kwadayin mutane ya jawo shi, wasu kuma suka yi bakin ciki kan matsayinmu, alhali hukunci na Allah ne, kuma makoma a ranar kiyama tana nan gareshiâ€‌. Ya fadi wannan a jawabin wanda ya tambaye shi: Yaya mutane suka ture ku daga wannan matsayi alhali ku kuka fi cancanta da shi.

Sannan sai imam Ali ya cigaba da magana kan wani abin da ya fi ban mamaki na wannan zamani da kamar Mu’awiya zai zo yana jayayya da shi, yana mai cewa “Zamani ya kai munzalin da yanzu ya ba shi dariya bayan ya sa shi kukaâ€‌[46].


 

Game Da Ahlul Baiti (A.S)

Kamar yadda ya bayyana a fili na karfafa wa ga hakkinsa musamman, matsayin Ahlul Baiti (A.S) yana iya bayyana garemu daga wadannan kalmomi da suka zo daga gareshi:

1- Fadinsa: “Haka yake, duniya ba za ta taba zama ba hujjar Allah ba a cikinta, ko zahiri mash’huri ko kuma boyayye, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baceâ€‌[47]. Ibn Abil Hadid malamin sunna ne amma yana cewa: A nan Imam Ali (A.S) ya yi nuni da bin mazhabar Shi’a isna ashariyya ne[48].

2- Fadinsa: “Ba a kwatanta alayen Muhammad da wani daga wannan al’umma su ne asasin addini kuma madogarar yakini… su ne suke da hakkin wilaya da jagoranci, kuma wasiyya da gado nasu neâ€‌[49].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next