Imamanci Da Nassi2



Wannan kuwa ita ce mahangar da yawa daga sahabbai, wadanda suka tafi a kan hakan sun hada da, Abu Sa’idul Khuduri, da Anas dan Malik, da Wasila dan Aska’a, da Ummul muminin Ummu Salama, da A’isha, da Ibn Abi Salama -agolan Annabi- da Sa’ad dan Abi Wakkas, da sauransu.

Ma’abota tafsiri da ruwayar hadisai da dama sun tafi a kan hakan daga cikinsu akwai; Faharur razi a littafin Tafsirul kabir, da Zamakhshari a Kusshaf, da Kurdabi a Aljami’u li ahkamil kur’an, da Shaukani a Fatahul gadir, da Tabari a Jam’ul bayan an tawili ayil kur’an, da Suyudi a Durrul mansur, da Ibn Hajar Al’askalani a littafin Isaba, da Hakim a Mustadrak, da Zahabi a cikin Talkhis, da imam Ahmad dan Hanbal a littafin Masnad.

Wannan kuwa shi ne ra’ayi da yafi zama daidai, shi ya sa ma zamu gani a ruwayar Muslim a sahihinsa da sanadinsa zuwa ga Amir dan Sa’ad dan Abi Wakkas, daga babansa ya ce: Mu’awiya dan Abi Sufyan ya umarci Sa’ad da ya tsinewa imam Ali (A.S) ya ce: Me ya hana ka ka zagi Aba turab? -Kinaya ce ta imam Ali- Sai Sa’ad ya ce: Amma matukar ina tuna uku da Manzo ya fada game da shi ba zan taba zaginsa ba, wallahi ya zama ina da daya daga cikinsu ya fi mini jajayen dabbobiâ€‌.

Na ji Manzo (S.A.W) yana cewa da shi -yayin da ya bar shi a wani yaki- sai Ali ya ce: Ka bar ni tare da mata da yara? Sai Manzo (S.A.W) ya ce da shi: Ba ka yarda ba da cewa matsayinka a wajena kamar matsayin Haruna ne gun musa sai dai babu wani Annabi bayana.

Na kuma ji shi (S.A.W) yana fada a ranar Haibar: Zan bayar da wannan tuta ga wani mutum da yake son Allah da manzonsa, Allah da manzonsa suke sonsa, ya ce: Sai duk muka yi burinta, sai ya ce: Ku kira mini Ali, sai aka zo da shi yana ciwon ido sai ya yi tofi a idanunsa sannan ya mika masa tutar da Allah ya bayar da nasara a hannunsa.

Yayin da ayar Mubahala: “Ka ce ku zo mu kira â€کya’yanmu da â€کya’yanku…â€‌ ta sauka sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain ya ce: Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidanaâ€‌[80].

Tirmizi ya rawaito a sahihinsa da sanadinsa daga Amir dan Sa’ad dan Wakkas ya ce: Yayin da wannan aya ta sauka “Mu kira â€کya’yanmu da â€کya’yankuâ€‌ sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain sannan ya ce: Ya Allah wadannan su ne Ahlin gidanaâ€‌[81].

Haka nan Hakim[82] ya rawaito shi a littafin Mustadrak da Baihaki[83] shi ma a littafin sunna.

Mawallafi littafin Kusshaf yana cewa: Babu wani dalili mafi karfi ga falala da daukaka da ya kai wannan ga ma’abota bargo, wadanda su ne Ali da Fadima da Hasan da Husain. Domin su yayin da yayar mubahala[84] ta sauka ya kira su ya rungume Husain ya rike hannun Hasan, Fadima tana bayansa Ali kuma yana bayanta, da wannan ne aka san ma’anar ayar, kuma â€کya’yan Fadima da zuriyarsu ana kiransu â€کya’yansa, kuma ana danganta su ga Manzo dangantawa ingantacciya mai amfani a duniya da lahira[85].

Imam Ahmad ya rawaito a babin falala da sanadinsa daga Shaddad Abi Ammar, ya ce: Na shiga wajan Wasila dan Aska’a, a wajansa akwai wasu mutane sai suka rika maganar Ali (A.S) sai suka zage shi ni ma sai na zage shi tare da su, bayan sun tashi sai ya ce da ni: Ba na ba ka labari ba daga abin da na gani daga manzon Allah (S.A.W) ? Sai na ce: Na’am, Sai ya ce: Na zo wajan Fadima (A.S) ina tambayar ta Ali, sai ta ce ya tafi wajan manzon Allah (S.A.W), sai na zauna na saurare shi har sai da manzon Allah ya zo a tare da shi akwai Ali da Hasan da Husain (A.S), kowannensu yana rike da hannunsa, sai ya zaunar da Hasan da Husain kowanne a kan cinyarsa sannan sai ya lulluba masu tufafinsa -ko kuma bargo- sannan ya karanta wannan aya: “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya tsarkake ku tsarkakewaâ€‌. Sannan sai ya ce: “Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidana, Ahlin gidana su suka fi cancantaâ€‌[86]. Tabari ya rawaito shi a cikin tafsirinsa[87] da Tirmizi[88] a cikikn sahihinsa, da Suyudi[89] a Durrul mansur, da Haisami a Majma’az zawa’id[90], da Hakim a Mustadrak[91] da Ahmad a Masnad[92].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next