Imamanci Da Nassi2



7- Hadubar shakshakiyya wacce take da karfafuwa daga malamai[33] daban-daban kuma take da ma’ana da take nuni ga hakan a fili dalla-dalla:

“Amma wallahi! Hakika wane ya sanya ta (rigar halifanci) alhalin kuma ya san cewa misalin matsayina game da ita kamar matsayin kan inji ne na nika da dutsensa, kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni yake gangarowa kuma tsuntsu ba ya iya kaiwa wajena (duk tashinsa), amma sai na sakaya tufafi na kau da kai[34] na kuma cije na kawar da kai, na zama ina mai kai-kawon ko in tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu…!

Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa! har sai da na farko ya wuce, sai ya mika ta zuwa ga wane bayansa…

Abin mamaki! Yayin da ya kasance yana neman ya sance ta daga wuyansa[35] a rayuwarsa sai ga shi ya kulla (mika) ta ga wani bayan wafatinsa, ya mamakin tsananin yadda suka yi kashe mu raba na abin da yake cikin hantsarta…![36]

Sai na yi hakuri tsawon lokaci, da tsananin jarabawa, har sai da ya wuce shi ma sai ya sanya al’amarin halifanci a hannun wasu jama’a da ya raya cewa (wai) ni daya ne daga cikinsu, Kaicon al’amarin shura!, yaushe ne kokwanton fifikon al’amarina a kan na farkonsu ya faru har da zan zama ana sanya ni tsaran makamantan wadannan!…â€‌[37].

Daga wannan magana ta imam Ali (A.S) zamu sani cewa; ashe kenan Abubakar ya san matsayin imam Ali na halifanci da daukakarsa kamar yadda kan dutsen markade da nika yake da daukaka a kan jikin dutsen ne.

Saoba haka ne yake a fili cewa matsayinsa ba boyayye ba ne sai dai mun ga tarihi yan neman ya farar da wani abu na jayayya domin ya yi daidai da abin da ya faru a tarihi, kamar yadda muka samu wasu suna neman musun maganarsa a game da halifanci, wanda da can sun yi musu ga hadisan Manzo (S.A.W). Amma gaskiya tana nan, sai dai abin takaici da tarihi bai karkata zuwa ga Ali ba! Tarihin da ya riga ya tabbatar da cewa imam Ali bai yi bai’a ga Abubakar sai bayan wata shida, sai ya nemi toshe kunnensa game da wannan jinkiri da imam Ali ya yi!

8- Maganarsa bayan shura, yayin da suka yi wa Usman bai’a yana mai cewa: “Wallahi kun sani ni na fi cancanta fiye da wanina, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya kubuta zalunci ya kasance a kaina ne ni kadai, domin neman ladan Allah da falalarsa, da kuma nisantar abin da yake kuna goggoriyonsa na kawa da adonsaâ€‌[38].

Ibn Abil Hadid ya samu wannan kalma cikin karshen abin da Ali ya fada a wannan lokaci a maganar da ya nakalto ta a nan bayan ya kawar da duk wani kokwanto game da ingancinta, sai ya ce: Mu muna ambaton wannan abu da ya zo na ruwayoyi masu yawa na imam Ali da ya hada ma’abota shura da Allah, kuma mutane da dama sun rawaito wannan da yawa, amma abin da ya inganta bai kasance da tsawo ba kamar yadda aka rawaito, sai dai bayan sun yi bai’a ga Usman shi ya ki bai’a ya ce: “Mu muna da hakki da in an ba mu sai mu karba, amma idan aka hana mu shi sai mu hau bayan rakuma komai nisan tafiyaâ€‌.

Sannan sai ya ce da su: “Ina hada ku da Allah shin a cikinku akwai wanda Manzo ya sanya shi dan’uwa tsakaninsa da shi in ba ni ba?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next