Imamanci Da Nassi2



Amma Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Biyu

Hadisin da Manzo (S.A.W) ya fadi adadin imamai a ciki kuma su sha biyu ne; Manzo ya bayar da labarin adadin imamai da zasu zo bayansa da imami kuma halifa bayansa kamar yadda ma’abota sihah (ingantattun littattafai) da ma’abota masanid suka rawaito kamar yadda zai zo:

1-Muslim ya raywaito daga Jabir daga Samura cewa ya ji Annabi (S.A.W) yana cewa: “Addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa har sai alkiyama ta tashi ko kuma an samu halifofi goma sha biyu a gareku dukkaninsu daga Kuraishâ€‌. A wata ruwaya sai Annabi ya fadi wata kalma da ban ji ba, sai na tambayi babana: menene manzon Allah ya ce: Sai ya ce: “Dukkaninsu daga Kuraishi sukeâ€‌[93].

A wata ruwaya ya ce: “Dukkaninsu daga Bani Hashimâ€‌[94].

Ahmad da Hakim sun rawaito da lafazin Hakim daga Masruk ya ce: Mun kasance muna zaune a wani dare gun Abdullahi dan Mas’ud yana karanta mana Akur’ani sai wani mutum ya tambaye shi: ya Aba Abdurrahman shin kun tambayi Annabi (S.A.W) halifa nawa ne zai mallaki al’amarin wannan al’umma? Sai Abdullahi ya ce: Tun da na zo Iraki ba wanda ya tambaye ni wannan kafin kai! Sai ya ce: Mun tambaye shi sai ya ce: “Goma sha biyu ne, da adadin zababbun Bani Isra’ilâ€‌[95].

Dimuwar Da Suka Samu Game Da Fassarar Hadisin

Malaman makarantar halifofi sun samu dimuwa wajan bayanin abin da ake nufi da goma sha biyu a wannan ruwaya da aka ambata, kuma zantuttukansu suna karo da juna.

Ibnl Arabi ya fada a sharhin sunan Tirmizi: Sai muka kirga bayan Manzo (S.A.W) sai muka samu sarakuna goma sha biyu sai muka samu Abubakar, Umar, Usman, Ali, Hasan, Mu’awiya, Yazid, Mu’awiya dan Yazid, Marwan dan Hakam, Abdulmalik dan Marwan, Walid, Sulaiman, Umar dan Abdul’Aziz, Yazid dan Abdulmalik, Marwan dan Muhammad dan Marwan, Assaffah…

A nan sai ya kirga halifan ishirin da bakwai na Abbasawa zuwa zamaninsa sannan sai ya ce: Idan muka kirga goma sha biyu, adadin ya kare daga Sulaiman amma idan muka kirga su da daukaka to akwai biyar daga halifofi wato halifofi hudu da Umar dan Abdul’Aziz amma ni kam ban gane wani abu ba game da wannan hadisi[96].

Alkali Iyad yana fada game da amsar wani wanda ya ce: adadin da suka yi mulki sun wuce hakan. Da cewa; wannan magana ba ta da hujja, domin Manzo bai ce goma sha biyu ne kawai zasu yi mulki ba, don haka ba abin da zai hana su fi hakan yawa[97].

Shi ma Suyudi yana bayar da amsa game da hakan ya ce: Abin da ake nufi da sha biyu ana nufin halifofi sha biyu a dukkan zamanin musulunci har zuwa ranar alkiyama da zasu yi aiki da gaskiya koda kuwa ba a jere suke ba[98].

A littafin Fathul Bari: Halifofi hudu sun gabata kuma ba makawa da cikon saura kafin alkiyama ta tashi[99]. Ibnul Jauzi ya ce: A kan haka abin nufi da sannan sai bala’i ya faru ita ce fitina da zata faru kafin alkiyama na daga bayyanar Dujal da abin da zai biyo baya[100].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next