Imamanci Da Nassi2



Yayin da Manzo (S.A.W) ya dawo daga hajjin bankwana, sai wahayi ya sauka a kansa yana mai tsananta masa: “Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah ne yake kare ka daga mutaneâ€‌[8], sai ya tsayar da jama’a gun Gadir khum, ya tara mutane a tsakiyar rana, ga zafi mai tsanani, ya yi musu huduba yana mai cewa: “An kusa kira na sai in amsa kuma ni mai bar muku sakalaini ne, daya ya fi daya girma, littafin Allah da zuriyata. a ruwayar Muslim[9] da Ahlin gidana ku duba yadda zaku maye mini a cikinsu, domin su ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tafkiâ€‌. Sannan sai ya ce: “Hakika Allah shugabana ne kuma ni shugaban duk wani mumini neâ€‌. Sannan sai ya kama hannun Ali ya ce: “Duk wanda nake shugabansa to wannan shugabansa ne[10] ya Ubangiji ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, ka taimaki wanda ya taimake shi[11], ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juyaâ€‌[12].

Kuma hakika saukar wahayi da wannan aya ya biyo bayan faruwar wannan abu mai girma da fadin Allah (S.W.T): “A yau ne na kammala muku addininku na kuma cika ni’imata a gareku na yardar muku da musulunci shi ne addiniâ€‌[13],

Wasu hadisai da aka rawaito daga Manzo suna cewa, bayan saukar wannan aya a wannan rana abar halarta wacce ita ce ranar sha takwas ga watan zil-hajji[14] ranar Gadir sai ya ce: “Allah mai girma! Godiya ta tabbata ga Allah a kan kammala addini da cika ni’ima da yardar Ubangiji da manzancina da kuma shugabancin Ali bayanaâ€‌[15].

A ruwayar Ahmad: “sai Umar dan khaddabi ya gamu da shi –imam Ali- bayan nan, sai ya ce da shi: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Dalib, ka wayi gari ka maraita shugaban dukkan mumini da muminaâ€‌[16].

Ba mu samu wani abu ba a rayuwar Manzo (S.A.W) da yake ambaton wani abu da zai iya tabbatar da cewa Manzo ya nufi tabbatar da al’amarin halifanci bayansa in banda nazarin wasiyya a matsayinta na sakon shari’a, ba a matsayin jagoranci na siyasa ba kawai, shi al’amari ne da yake Ubangiji ne da yake aiwatar da zabar abin da ya so na sakon manzancin Annabi (S.A.W) yayin da Kur’ani ya yi nassi a kan Annabi da cewar, idan bai isar da wannan al’amari na sakon halifanci da shugabanci bayansa ba, da bai isar da komai na sakon da ya dauki shekara ishirin yana wahala a kan isar da shi ba[17].

Abin da Ake Tsammani DaAbin daYa Faru A Tarihi

Shahid Sadar (K.S) ya yi muhawarar wannan mas’alar da ta faru a tarihi da bayanai kamar haka; Tsammanin cewa Manzo (S.A.W) ya riki wata hanya ta barin mutane ba magaji ba halifa, da ma’anar cewa Manzo bai taba tarbiyyantar da mutane a kan al’amarin halifanci ba da jagoranci bayansa, wannan kuwa batacce ne domin ya yi karo da matasyin Annabi wanda yake sane da dukkan makomar sakon da ya zo da shi, sannan ya ci karo da hadisai da suka yi Magana game da muhimmancin al’amarin al’umma bayansa a rayuwarsa da kuma kafin wafatinsa a karshen rayuwarsa[18].

Kamar yaddda shahid Sadar ya soke ra’ayi na biyu wanda yake ganin shura da fadinsa: Abin da aka samu daga Manzo da muhajirai da Ansar ya kore batun shura. Domin da Annabi ya dangana al’amari zuwa ga hannun Muhajirun da Ansar bai taskace shi da Ahlin gidansa (A.S) ba, da wannan al’amari ya zama daga mafi bayyanar al’amura da kuma ya wayar da kan al’mmma a kan tsarin shura da bayaninsa dalla-dalla domin mutane su san yadda tsarinta yake.

Da Annabi (S.A.W) ya wayar da su a kan haka, to da kuma an samu bayyanar wannan a cikin hadisansa da suke rawaitowa daga gareshi da take dauke da bayani game da shura. Amma sai ya zama ba mu samu wani wanda yake dauke da wannan tunani ba, sai ya zama al’ummar Muhajirun da Ansar duka mun same su ne jama’a guda biyu mabanbanta.

Na daya: Jama’ar da Ahlul Baiti suke jagoranta mai dauke da tunanin wasiyya da Manzo (S.A.W) ya yi game da halifancinsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next