Imamanci Da Nassi2



Buhari yana cewa: “Ali (A.S) ya ki yin bai’a ga Abubakar tsawon wata shida har sai da Fadima (A.S) ta rasuâ€‌[64]. A hadubar imam Ali (A.S) ya fadi dalilin da ya sa ya yi bai’a, a hudubarsa da yake cewa:

A- “Na rantse da Allah ba domin tsoron rarraba ba, kafirci ya dawo, addini ya rushe, da mun kawar da wannan jagoranci, amma sai muka yi hakuri a kan wasu zogi da bakin ciki da yake damun muâ€‌[65].

B- Yana fada a Nahajul Balaga: “Sai na duba, sai ga shi ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu, na kuma runtse idanuna a kan wannan kwantsa, na yi himmar hadiyar bakin ciki, na yi hakuri a kan juriya da kuma hakurin dacin da ya fi na madaciâ€‌[66].

Shin zai yiwu a zo da wani bayani wanda ya fi wannan zama karara?! In ba haka ba menene ya sa duk wannan bayan irin wannan kokawa da kai kara? alhalin shi ne mafi sanin mutane da halin da ake ciki da sakamakon abin da ya faru.

Da a ce bai kafa musu hujja ba ya baro janazar Manzo (S.A.W) ya tafi Sakifa ya bar jikin masoyinsa (S.A.W) bai wanke shi ba, ya zo ya dora hannunsa a kan hannunsu ya yi bai’a da ba ma’ana ya zo da irin wannan kafa hujja. Idan ya tabbata ta hanya sahihiya Ali dan Abi Dalib (A.S) cewa ya soki nazarin shura ya kuma shelanta cewa ta saba wa shari’a… ya kuma fadi cewa an tilasta shi ne ya yi bai’a ga halifofi uku to bai’arsa ba ta da wani dalili na shari’a a kan halifancinsu kamar yadda wannan ya tabbata a fili daga maganganunsa.

Sannan ya bayyana cewa shi ne ya fi cancanta da halifanci, shin zai yiwu mu ce cancantarsa ga halifanci tana nufin shi ya fi, da ma’anar cewa duk da shi ne ya fi amma da waninsa zai karbi halifanci da ba komai? ko kuwa tana nufin shi ne kawai ya cancanta da halifanci?

Wannan ra’ayi na farko ba daidai ba ne saboda nassin hadisai da kuma maganganun imam Ali (A.S) yayin da yake cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar alhalin ni ne na cancanci in sanya rigata wannan (wato in yi halifanci) daga garesuâ€‌. Wannan yana nufin cancantar da ta kebanta da shi, ba wai yana nufin fifikon cancanta ba ta yadda wani ma yana iya cancanta da ita, domin ba ma’anar ya ce rigarsa ce sannan ya zama ba ya nufin cancanta, domin mai riga shi ne mai ita mai cancanta da ita mai mallakarta.

Sannan ga fadinsa da yake cewa: “…Na zama ina mai kai-kawon ko ina tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu, da babba yake tsufa a cikinsa yaro kuma yake girma a ciki, mumini yake shan bakar wahala a ciki har sai ya riski Ubangijinsa.

 Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai nayi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kumashakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewaâ€‌[67].

Ma’anarsa sai na samu kaina tsakanin ko in karba da karfin da bai isa ba kamar yadda ya zo a fadarsa (A.S): “Saina duba, sai gaba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) saina yi wa mutuwa rowarsuâ€‌. Wato daya sami karfi isasshe da ya yaki ma’abota Sakifa kamar yadda yake a maganarsa da aka sani da yake cewa: “Da nasamu mutum arba’in masuniyya da gaskiya da na kawar da mutunenâ€‌.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next