Imamanci Da Nassi2



Na biyu: jama’ar mutanen Sakifa da suke bin halifanci da ya biyo bayan wafatin Manzo (S.A.W).

Kuma a dukkaninsu ba wanda yake dauke da tunanin shura kamar yadda tarihi ya nuna, yayin da Abubakar ya yi wasiyya da halifancin Umar bai nemi shawarar kowa ba sai ya dora shi kan halifanci a kan al’umma ba tare da shawarar musulmi ba, ko shugabanninsu, sai Umar shi ma ya tafi a kan wannan tafarki ya zabi wasu wadanda zasu zabi wani daga cikinsu, ya kasance yana cewa: “Da Salim ya kasance rayayye da ban sanya ta shura baâ€‌, wannan kuwa bayani ne karara daga gareshi da rashin imaninsa da shura[19].

Da Annabi ya dauki matakin ya sanya ta shura a tsakanin mutane da ya sanya wannan a da’awarsa tun farko domin ya sanar da wannan al’umma al’amarin sakon Allah da zai iya ba ta damar fuskantar duk wata matsala ta tunani da fikira da wannan kira zai iya fuskanta, yayin da ake samun karuwar budi da shigowar al’ummu jama’a daban-daban.

Sai ya zama ba mu samu komai ba dangane da wannan, kuma abin da aka sani daga sahabbai sun kasance suna jin nauyin fara tambayar Manzo (S.A.W), kai har ma sun bar rubuta sunnar Manzo (S.A.W) duk da kuwa ita ce madogara ta biyu ta shari’a bayan Kur’ani, tare da cewa rubutawa ita kawai ce hanyar da ta rage domin kiyaye ta.

Kuma tarihi ya tabbatar da cewa â€کya’yan Muhajirun da Ansar ba su da komai a hannunsu na daga abin da ya shafi ilimi game da mas’aloli masu yawa, sai ga shi hatta da kasar da ake ci yaki halifa ba shi da wani hukumci na shari’a game da ita a hannunsa da ya sani; ko a raba ta tsakanin mayaka? ko ta zama wakafi ga dukkan musulmi? Kai har ma sun yi sabani a kan yawan kabbarorin sallar mamaci, wasu suna cewa Manzo ya yi biyar, wasu suna cewa ya yi hudu ne.

Haka nan ya bayyyana a fili cewa Manzo bai kawo shura ba, sai ya zama ba abin da ya rage sai hanya ta uku wacce take cewa Manzo (S.A.W) ya shirya imam Ali da umarinin Allah ya kuma sanya shi halifansa a kan sako da al’umma bayansa a matsayinsa na mai masaniya da zurfin abin da wannan sako ya kunsa da kuma iko a kan kula da tafiyar sakon da cigabansa bayan Manzo (S.A.W), kamar yadda ya tabbata a tarihi a shekaru talatin da ya yi bayan wafatin Manzo (S.A.W) da furucin masu tarihi.

Kuma duk abin da da ya zo na hadisai mutawatirai game da Ahlul Baiti (A.S) ba komai ba ne sai karfafa wa ga wannan hanya ta uku, wato ayyana halifansa da umarnin Allah[20].

Nassin Wasiyya A HadisanImam Ali Da Ahlul Baiti

 Abu ne a fili ga wanda ya karanta tarihi cewa imam Ali shi ne wanda ya bayyanar da hadisai da suke nuna halifancinsa bayan Manzo da sunansa (A.S). Kuma ingancin wannan wani abu ne da ma’abota ilimi na wannan al’umma da suka fitar da son rai daga zukatansu suka tabbatar da shi, kuma sama da malami hamsin daga masu sharhin hadisansa sun yi bayanin haka suka kuma kare wannan kariya mai cike da hujjoji da dalilai da suka bayar da nutsuwa a kan hakan[21].

Ali (A.S) shi ne wanda ya dawo wa kwakwalen mutane batun hadisan halifancinsa ba tare da wata jayayya ba, bayan an hana fadin wadannan hadisai a lokacin halifofi da suka gabace shi, yayin da suka hana fadin hadisan manzon Allah sai wanda ya shafi ibada kawai:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next