Imamanci Da Nassi2



ManzoYa Yi Aiki Domin Karfafa Nazarin Nassi

Idan muka kula da nazari ta fuskancin tarihi muka kuma lura da matakan da Annabi ya dauka wajan tarbiyyar al’umma da wayar da ita game da al’amarin Ubangiji wanda ya shafi halifanci sai mu samu cewa ya karfafa nazarin nassi a kwakwalenmu ne ba shura ba, kuma ba a samu wani waje da Manzo ya ambaci wayar da al’umma da tarbiyyantar da ita a kan nazarin shura ba tun daga saukar fadin Allah madaukaki “Ka gargadi jama’arka makusantaâ€‌. Har zuwa saukar fadinsa madaukaki: “Ya kai wannna Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka, idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah yana kare ka daga mutaneâ€‌.

Hakika ya zo daga dan Abbas daga imam Ali (A.S) cewa ya ce: “Yayin da wannan aya ta sauka; “Ka gargadi jama’arka makusantaâ€‌ ga manzon Allah (S.A.W) sai ya kira ni ya ce: Ya Ali Allah ya umarce ni da in gargadi jama’ata makusanta, sai na samu kunci na san cewa idan na bayyana wannan al’amari to zan ga abin ki daga garesu, sai na kame gabarinsa sai Jibril ya zo mini, ya ce: Ya Muhammad idan ba ka yi abin da Allah ya umarce ka to zai azabtar da kai, saboda haka ka yi mana abinci sa’i daya, ka kuma sanya karfatar akuya, ka cika mana kwano na nono, sannan ka kira duk Bani Abdulmudallib domin in yi musu magana in isar musu da sakon da aka umarce ni da shi, sai na aikata abin da ya umarce ni da shi, sannan na kira su, a wannan lokaci mutum arba’in ne da daya ko ba daya, a cikinsu akwai ammominsa abu Dalib, da Hamza, da Abbas, da Abu Lahab, Ya ce: Sai manzon Allah (S.A.W) ya yi magana ya ce: Ya Bani Abdulmudallib ni wallahi ban san wani saurayi a larabawa da ya zo wa mutanensa da mafifici daga abin da na zo muku da shi ba, ku sani ni na zo muku da alherin duniya da lahira, kuma hakika Ubangiji ya umarce ni da in kira ku zuwa gareshi, wanene a cikinku zai karfafe ni a kan wannan al’amari a kan ya kasance dan’uwana wasiyyina kuma halifata a cikinku?, Imam Ali ya ce: Sai duk mutanen suka tage gaba daya, sai na ce alhalin ni ne na fi kowa karancin shekaru a cikinsu, ni ne ya Annabin Allah zan zama mai taimakon ka a kansa. Sai ya riki kafadata sannan ya ce: Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina halifata a cikinku ku ji ku bi daga gareshi, Ali (A.S) ya ce: Sai mutanen suka tashi suna dariya suna cewa da Abi Dalib, ya umarce ka ka ji daga danka kuma ka bi shiâ€‌[1].

Haka nan Manzo Allah (S.A.W) ya fara shirya wa al’umma tun daga farawa da makusantansa yana mai nuna wa al’umma halifancin Ali (A.S) bayansa, yana mai wasiyya a kan dan’uwansa da wasiyya da halifanci da kuma wajabta biyayya gareshi, Annabi ya kasance yana mai bayyyana ma’anar ayoyin Kur’ani da suke sauka a kansa game da hakkin Ali musamman ayoyin da suka shafi halifanci da imamanci.

Zamakhshari a tafsirinsa yana fada game da fadin Allah (S.W.T): “Kawai shugabanku Allah ne da manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsayar da salla suke bayar da zakka alhalin suna masu ruku’iâ€‌[2], Wannan aya ta sauka game da imam Ali (A.S) yayin da wani ya tambaye shi yana mai ruku’u a cikin salla sai ya jefa masa zobensa[3].

Domin kawar da rikitarwa da kuma yanke duk wani tawili game da abin da ake nufi da kalmar wali da kuma nuna ko waye a wannan waje sai Annabi (S.A.W) ya bayyana a wajaje da dama cewa: “Ali daga gareni ne, ni ma daga gareshi nake, kuma shi ne shugaban duk wani mumini bayanaâ€‌[4].

Saboda karfafa shuganbacin imam Ali (A.S) da kuma matsayinsa mai muhimmanci a wajan bayyana sakon musulunci da kuma cimma hadafofin ta hanyar aiwatar da jagoranci domin aiwatar da hukunce-hukunce, da kuma kare su daga dukkan abin da zai iya karkatar da su da kuma canja su bayan Manzo, sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ali daga gareni yake ni ma daga Ali nake, kuma ba mai bayar wa daga gareni sai ni ko Aliâ€‌[5].

 Kuma Manzo (S.A.W) ya karfafa wannan ma’ana a aikace, a bayyane, da rana, a kissar isar da sako a surar bara’a, kuma Ahmad dan Hanbal ya fitar da wannan ruwaya a Masnadinsa daga Abubakar yayin da ya ce: “Annabi ya aika ni da bara’a zuwa mutanen Makka, sai ya tafi kwana uku sannan sai ya ce da Ali: Ka yi maza ka riske shi, sai Abubakar ya mayar da ita gareni na isar da ita, yayin da Abubakar ya zo wajan Manzo (S.A.W) sai ya ce: Ya manzon Allah shin wani abu ne ya faru game da ni?! Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ba komai game da kai sai alheri, sai dai ni an umarce ni da kada wani ya isar da sako daga gareni sai ni ko wani mutum daga gareni[6].

A littafin Kusshaf: Abubakar ya rawaito cewa: Yayin da yake kan hanya domin isar da surar bara’a sai Jibril (A.S) ya sauka ya ce: “Ya Muhammad kada wani ya isar da sakonka sai wani mutum daga gareka, sai ya aika Aliâ€‌[7].

Daga karshe Kur’ani ya cika wannan maudu’i mai muhimmanci wanda ya shafi haifar da tunani da tarbiyyantarwa a kan yadda al’amarin shugabanci da halifanci zai kasance bayan Manzo (S.A.W) a karshen abin da ya sauka garshi a ayar tablig sannan da kuma ayar cika addini bayan kissar Gadir mash’huriya ta yadda babu wani uzuri ga mai kawo uzuri, Kissar Gadir kissa ce da dayawa sun rawaito ta da dan sabani kadan a wasu wurare Kamar yadda zai zo:



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next